Kano: Kotun Ta Tsare Matashi Kan Zargin Caka Wa Abokinsa Wuka a Ciki, Wanda Ake Zargi Ya Magantu

Kano: Kotun Ta Tsare Matashi Kan Zargin Caka Wa Abokinsa Wuka a Ciki, Wanda Ake Zargi Ya Magantu

  • An gurfanar da wani matashi a gaban babbar kotun jihar Kano kan zargin ta'addanci wa abokinsa kan 'yar hatsaniya
  • Wanda ake zargin, Misbahu Yau ya caka wa Kamalu Sadik ne wukar har sai da hanjin cikinsa ya fito
  • Ana zargin Misbahu ya caka wa Kamalu Sadik ne wukar bayan sun samu wata hatsaniya a tsakaninsu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da wani matashi a gaban babbar kotun jihar kan zargin caka wa abokinsa wuka a ciki.

Wanda ake zargin, Misbahu Yau ya caka wa Kamalu Sadik ne wukar har sai da hanjin cikinsa ya fito.

Kotu ta tsare matashi a Kano kan zargin cika wa abokinsa wuka
Ana zargin matashin da cika wa abokinsa wuka kan wata 'yar hatsaniya. Hoto: Court of Appeal.
Asali: UGC

Wane hukuci kotun ta yanke a Kano?

Kara karanta wannan

An daure matashi shekaru 75 a gidan kaso kan zargin damfarar biliyan 1, ya yi ta maza

Kotun da ke zamanta a kan hanyar Miller da ke birnin Kano ta tsare matashin har sai an kammala bincike, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da mai gabatar da kara, Barrister Lamido Abba Sorondinki ya karanto tuhume-tuhume kan wanda ake zargi, ya musanta aikata laifukan.

Sorondinki daga bisani ya roki kotun ta dage ci gaba da sauraran karar har sai sun gabatar da shaidu.

Wane mataki alkalin kotun ya dauka kan shari'ar?

Lauyan wanda ake zargi, Ahmed Ali bai kalubalanci bukatar Sorondinki ba sai dai ya bukaci ba shi takardun da za su gabatar a kotun.

Alkalin kotun, daga bisani ya umarci ci gaba da tsare wanda ake zargi har ranar 28 ga watan Faburairun 2024, Latest News Nigeria ta tattaro.

A kwanakin baya ma, EFCC ta cafke wani manajan kamfani a Kano kan badakalar miliyoyin kudade na kamfanin a kokarin samar da iskar gas.

Kara karanta wannan

Labari Mai Zafi: Kotun koli ta tsaida ranar sauraron shari’ar zaben Gwamnan Kano

EFCC ta cafke matashi kan zargin damfara

A wani labarin, Hukumar EFCC reshen jihar Oyo ta gurfanar da wani matashi kan zargin damfarar naira biliyan daya.

Wanda ake zargin, Olaniyan Gbenga ya damfari jama'a da dama da nufin kwasar ganima a kamfaninsa da ake zuba hannun jari.

Daga bisani, kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 75 a gidan kaso ba tare da zabin biyan tara ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.