Bidiyon Yahaya Bello yana yi wa ɗan kwangilar China kaca-kaca akan ha'inci ya ɗauki hankulan mutane

Bidiyon Yahaya Bello yana yi wa ɗan kwangilar China kaca-kaca akan ha'inci ya ɗauki hankulan mutane

  • A ranar Litinin gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya tsawatar wa wani dan kwangila dan asalin kasar China
  • Hakan ya biyo bayan aikin da ya yi cike da ha’inci da kuma daukar tsawon lokaci kafin ya gabatar da shi
  • Gwamnan ya nuna rashin jin dadin shi ne a lokacin da yake zagayen duba ayyukan asibitin kwararru na jihar Kogi

Kogi - A ranar Litinin, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya tsawatar wa dan kwangilar China wanda yake da alhakin kammala ayyukan asibitin kwararru na jihar da ke Lokoja sakamakon yin ha’inci a aiki da kuma daukar lokaci mai tsawo kafin a kammala.

Bello ya nuna rashin gamsuwar sa da aikin yayin zagayen duba ayyukan da ake tsaka da yi a jihar, inda ya bayyana cewa gwamnatin jihar ba za ta amince da ayyukan ba kamar yadda NewsWireNGR ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Bidiyon Yahaya Bello yana yi wa ɗan kwangilar China kaca-kaca akan ha'inci ya ɗauki hankulan mutane
Bidiyon Yahaya Bello da ɗan kwangilar China. Hoto: NewsWireNGR
Asali: Facebook

Yayin da gwamnan ya ke kalubalantar kamfanin kasar Chinan, Changjiang Construction Nigerian Ltd, ya nuna takaicin sa karara da ha’incin da suka aiwatar ta hanyar yin ayyuka marasa nagarta.

Kamar yadda NewsWireNGR ta ruwaito, gwamnan ya ce:

“Ba ayi aikin komai ba! Kwamishinan ayyuka, kwamishinan lafiya, CMD, ban yarda da abinda nake gani ba kuma ban ga wani gyara ba anan. Hakan na nuna ba ku iya aiki ba.”
“Wannan bai kai nagartar GYB ba, ni mutum ne mai nagarta kuma duk aikin da zan aiwatar a jihar Kogi ina so ya zama mai nagarta kwarai, yadda duk inda aka kai za a san abin nan mai kyau ne.
“Ban gane ba, a wannan aikin ne nake ta kashe kudi kenan.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Arewa maso yamma ta rikice, kiyasin mu ya na kai da kai da Afghanistan

“Ya kamata a ce an kammala aikin nan tun kafin yanzu. Da farko kun dauki lokaci mai tsawo don haka kun saba wa yarjejeniyar da mu ka yi.”

Gwamnan ya bayar da lokacin da yake so a gyara kuma a kammala aikin

Gwamnan ya bayar da lokacin da za a kammala aikin ya kasance watan Disamba kuma a gyara komai yadda ya dace yayin da ya lashi takobin daukar mataki akan kamfanin da yake da alhakin kammala aikin.

Kamar yadda gwamnan ya ce:

“Wajibi ne ku san abin yi daga yanzu zuwa watan Disamba, idan ba haka ba zan dauki mataki akan ku. A gyara kuma a inganta komai yadda ya dace.
“Wannan ai shine kitso da kwarkwata kuma ba zan amince da hakan ba.
“Kuma zan tuhumi wanda ya gabatar wa da jihata ku a matsayin ‘yan kwangila saboda wannan ha’incin. Don ko wanda zai siyar muku da kayan aiki ban hada ku da shi ba.”

Kara karanta wannan

Nan da shekaru 2 za a kammala wurin kiwon shanun jihar Kaduna na N10bn, El-Rufai

“Wannan asibiti mai nagarta ne a kasar China? Idan ba ku da lafiya za ku so a kawo ku wannan asibitin? Ko kuma mun rike mu ku kudin aikin ku ne?
“Idan an taba irin wannan aikin a jihar Kogi ba karkashin GYB aka yi ba, kuma ba zan dauka ba.”

Gwamnan ya kara da zagaye wasu ayyukan da ke fadin jihar don tabbatar da yadda ‘yan kwangila suke aiwatar da ayyuka.

Bidiyon da ke nuna Yahaya Bello yana tsawatarwa yan kwangilan ya janyo hankulan mutane, wasu na ganin kamfen ne wasu kuma na ganin gwamnan ya damu da jiharsa ne shi yasa ya ke son a yi aiki mai kyau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel