Tinubu Ya Kadu Bayan an Fadi Tulin Bashin Najeriya Ma Su Tayar da Hankali, Bayanai Sun Fito
- Rahotanni sun bayyana yawan basukan da ake bin Najeriya masu tayar da hankali duk da halin da kasar ke ciki
- Hukumar Kula da Basuka a Najeriya (DMO) ta tabbatar da cewa a yanzu bashin kasar ya kai naira tiriliyan 87.9
- Legit Hausa ta ji ta bakin wani dalibi a bangaren tsangayar tattalin arziki kan basukan da ake bin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hukumar Kula da Basuka a Najeriya (DMO) ta tabbatar da cewa a yanzu bashin kasar ya kai naira tiriliyan 87.9.
Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a shafinta na X a ranar Alhamis.
Mene hukumar DMO ke cewa kan basukan Najeriya?
DMO ta kara da cewa wannan yawan basukan an lissafa su ne zuwa zango na uku na wannan shekara da mu ke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ce wannan ya kunshi karin kaso 0.61 daga cikin 100 idan aka kwatanta da yawan basukan a watan Yunin wannan shekara.
Basukan cikin gida sun karu da tiliyan 1.8 yayin da bashin waje ya ragu da dala biliyan 43.16 zuwa 41.59 a ranar 30 ga watan Yuni, cewar Vanguard.
Wace sanarwa DMO ta fitar kan basukan Najeriya?
Sanarwar ta ce:
"Jimillar yawan kudaden duka sun kai naira tiriliyan 87.91 a ranar 30 ga watan Satumba.
"Yawan kudaden kenan da ya kunshi basukan gida da waje na Gwamnatin Tarayya da kuma jihohi 36 da birnin Abuja."
Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya sake karbo wasu biliyoyin nairori bashi a kwanakin nan.
Legit Hausa ta ji ta bakin dalibin tsangayar tattalin arziki, Yusuf Abubakar Aliyu da ke Jami'ar jihar Gombe.
Yusuf ya yi Allah wadai da tarun basukan kasancewar ba a yi amfani da su ta hanyar da ya dace ba.
Ya ce duk bashi da ba a saka shi a bangaren ilimi ko kiwon lafiya da aikin gona ba to ba shi da amfani ga al'umma.
Ya ce:
"A gaskiya bayanan da DMO ta fitar game da bashin da ake bin Najeriya abin Allah wadai ne, kasancewar bashin ba a saka shi a gurbin da ya dace ba.
"Shi bashi kamata ya yi idan gwamnati ta ciwo ta saka shi a inda zai jawo hankulan masu zuba jari ciki da wajen kasa.
"Sannan a saka shi fannin da zai inganta rayuwar al'ummar kasa kamar Ilimi da kiwon lafiya da aikin gona da kuma bunkasa sanao'in hannu da sauransu."
Ya ce amma mu shugabannin mu sai su ciyo bashi su saka shi inda bazai amfani al'umma da komai ba wanda kuma dole sai an biya.
Tinubu ya nemi amincewar Majalisar don sake karbo bashi
A wani labarin, Shugaba Tinubu ya sake neman sahalewar Majalisa don sake runtumo bashin miliyan 400 daga Bankin Duniya.
Tinubu ya ce karbar bashin ya zama dole ganin yadda kasar ke bukatar kudade don karisa manyan ayyuka da aka fara.
Shugaban ya kasafta yadda za a kashe kudaden inda ya ce za a raba wa gidan miliyan 15 don rage musu radadin cire tallafin mai.
Asali: Legit.ng