Wike Ya Sanar da Mutane Su Tattara Kayansu, Zai Ruguza Gidaje 150-200 a Birnin Abuja

Wike Ya Sanar da Mutane Su Tattara Kayansu, Zai Ruguza Gidaje 150-200 a Birnin Abuja

  • Ministan harkokin birnin Abuja ya bada sanarwa cewa mutanen da ke zaune a yankin Nuwalege su bar gidajensu
  • Wani jami’in hukumar FCTA ya ce za a rusa gidajen da ke unguwar ne domin a samu wurin ginin hanyar jirgin sama
  • Rundunar sojojin sama su ka bukaci a tashi unguwar Nuwalege saboda jiragen saman fadar shugaban kasa su iya tashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A matsayinsa na babban Ministan harkokin birnin tarayya na Abuja, Nyesom Wike, ya sanar da mutanen Nuwalege su tashi.

The Nation ta ce Nyesom Wike ya bukaci masu zama a yankin Nuwalege da ke kan titin hanyar filin jirgin sama su bar unguwar.

Nyesom Wike
Nyesom Wike zai rusa gidaje a Abuja Hoto: @GovWike www.bigrentz.com
Asali: Twitter

Sanarwar ta fito ne daga bakin wani Dareka a FCTA, Mukhtar Galadima a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Tsaka mai wuya: Sama da 'yan Najeriya 1,000 aka damfara da sunan sama masu aiki a Burtaniya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A sa’ilin da yake tattaunawa da wasu mazauna, Mukhtar Galadima ya ce ya zama dole mutanen yankin su tashi domin za ayi aiki.

Darektan yake bayani a madadin Ministan na birnin Abuja cewa gwamnati za ta gina wurin tashin jirgin sama a unguwar Nuwalege.

Menene ya sa Wike zai tashi Nuwalege?

Ministan ya ce rundunar sojojin saman Najeriya ta aikowa ma’aikatarsa takarda tun a watan jiya cewa akwai bukatar yin wannan aiki.

Saboda haka dole za a tashi mutanen domin gidajensu ya shiga filin jiragen saman.

FCTA za ta rusa gidaje a birnin Abuja

"Daga cikin nauyin da yake kan mu, dole mu kira zama da al’umma da mazauna, shiyasa mu ke nan domin tattaunawa da kuma fada maku niyyarmu,
Domin zai zama rashin adalci idan mu ka dauka kayan aiki kurum mu ka fara cire gidaje."

Kara karanta wannan

Duka yarjejeniya 8 da aka dauka wajen sasanta Wike da Gwamna Fubara a Aso Rock

- Mukhtar Galadima

Abuja: Za a biya mutane hakkokinsu?

An rahoto Darektan yana cewa dalilin wannan aiki da za ayi, gidaje tsakanin 150 zuwa 200 ake sa ran za a rusa domin a samu sarari.

Galadima ya kyankyasa mazauna yankin za a biya bincike domin a biya wadanda su ka cancanta kudi domin su nemi wani wurin zaman.

Za a sasanta Nyesom Wike da Simi Fubara?

Ana da labari cewa a taron da aka yi a Aso Villa, Bola Tinubu ya yi wa Simi Fubara kaca-kaca saboda rusa ginin majalisar dokoki da ya yi.

Bayan an cin ma yarjejeniya, Gwamnan jihar Ribas, Mai girma Simi Fubara ya saduda da sunan zaman lafiya ake nema ba komai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng