Kujerar Gwamna Abba Ta Shiga Tangal-Tangal Bayan Malaman Addinin Musulunci Sun Yi Abu 1 a Kano
- Ƙungiyoyin malaman addinin Islama guda uku, Tijjaniyya, Izala, da Ƙadiriyya, suna goyon bayan Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC a kotun ƙoli
- Waɗannan malaman sun buƙaci kotun ƙoli da ta tabbatar da nasarar ɗan takarar gwamnan na jam’iyyar APC
- Malaman sun kuma gudanar da addu’o’i ga ɗan takarar jam’iyyar APC da alkalan kotun ƙoli kafin yanke hukunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Malaman addinin Musulunci daga manyan ƙungiyoyi uku a jihar Kano sun hallara a birnin domin gudanar da addu’o’i na musamman, inda suke neman nasara ga Nasiru Gawuna, ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2023.
Jaridar The Guardian ta ce a yayin taron, malaman sun kuma yi addu’o’i ga alkalan kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna da na kotun ɗaukaka ƙara, inda suka buƙaci a yi adalci kan ƙarar da jam’iyyar APC ta gabatar.
Ku tuna a baya kotun zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara sun tabbatar da Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gamayyar malaman addinin da suka haɗa da wakilai daga Tijjaniyya, Izala, da Ƙadiriyya, sun taru domin yin addu’o’in kariya ga alƙalan kotun zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara, rahoton Leadership ya tabbatar.
Sun nuna jin daɗinsu da abin da suke ganin maido da nasarar da aka wawushe wa mutanen Kano ga Gawuna, wanda aka amince da ya lashe zaɓen.
Malamai sun isar da muhimmin sako ga kotun ƙoli
A ƙarƙashin jagorancin Sheikh Albakry Mikail (Tijjaniyya), Malam Garba Yusuf Abubakar (Izala), da Farfesa Maibushira (Ƙadiriyya), Malaman sun buƙaci kotun ƙoli da ta yi nazari sosai kan abubuwan da aka gabatar tare da amincewa da Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano a hukumance.
Mallam Abubakar ya jaddada muhimmancin addu'a domin tabbatar da adalci a shari'ar.
A kalamansa:
"Mun taru a nan ne domin yin addu’o’i na musamman ga alƙalan kotun zaɓe da na kotun ɗaukaka ƙara."
"Hakazalika, muna kira ga alƙalan kotun ƙoli da su duba gaskiyar lamarin da ke gabansu, su yi wa al'ummar jihar Kano adalci, domin a kwato musu haƙƙinsu da aka sace."
An Yi Zanga-Zangar Nuna Goyon Baya Ga Gwamna Abba
A wani labarin kuma, kun ji cewa an gudanar da zanga-zanga a jihar Ogun domin nuna goyon baya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano.
Al'ummar Hausawa mazauna Sagamu a jihar Ogun sun fito kan tituna inda suka buƙaci Shugaba Tinubu da ya sa baki domin ganin an yi wa Gwamna Abba adalci.
Asali: Legit.ng