Dubun Makanike Ya Cika Bayan Cafke Shi Ya Na Siyar da Kayan Motar da Aka Ba Shi Gyara, an Yi Bayani

Dubun Makanike Ya Cika Bayan Cafke Shi Ya Na Siyar da Kayan Motar da Aka Ba Shi Gyara, an Yi Bayani

  • 'Yan sanda sun cafke wani matashin makanike da ke siyar da kayayyakin motar da aka ba shi gyara
  • Matashin da ake zargi, Adedamola Oluwaseyi mai shekaru 25 ya shiga hannu ne bayan rundunar ta samu bayanan sirri daga jama'a
  • Kakakin rundunar a jihar, Benjamin Hundeyin shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a jiya Litinin 18 ga watan Disamba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Rundunar 'yan sanda a jihar Legas ta cafke wani makanike kan zargin siyar da kayan motar da aka kawo masa gyara.

Wanda ake zargin, Adedamola Oluwaseyi mai shekaru 25 ya gudu da motar ce inda daga baya ya ke siyar da kayan motar daya bayan daya, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

To fah: Fitaccen malami ya ayyana shiga tseren takarar gwamna a jihar PDP, ya faɗi dalili

'Yan sanda sun cafke makaniki da ke siyar da kayan gyaran mota da aka ba shi
Rundunar 'yan sanda ta cafke makaniki da zargin siyar da kayan mota. Hoto: @LagosPoliceNG.
Asali: Facebook

Mene ake zargin makaniken da aikatawa?

Kakakin rundunar a jihar, Benjamin Hundeyin shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a jiya Litinin 18 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hundeyin ya ce an yi nasarar kama matashin ne bayan samun bayanan sirri daga mutane kishin kasa.

Ya ce:

"Rundunar 'yan sanda a jihar Legas ta kama wani matashin makanike mai shekaru 25 a Ladipo da ke yankin Mushin.
"Ana zargin matashin ta siyar da kayan motar da aka kawo masa gyara daya bayan daya.
"Cafke matashin ya faru ne bayan samun bayanan sirri da 'yan sandan ofishin yanki na Mushin su ka samu wanda su ka kai samame."

Wane martani 'yan sanda su ka yi?

An kama matashin da mota kirar Toyota wacce aka gane ta injin motar wanda ba ta da lamba kuma tayun gaba sun bata.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya dauko hanyar hana Shoprite barin Kano

Yayin da aka yi kawakkaran bincike, an gano wanda ake zargin ya tafi kasuwar Ladipo don siyar da kayayyakin motar.

Hundeyin ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin da zarar an kammala binciken da ake yi a kansa.

Kotun Koli ta tanadi hukuncin zaben Legas

A wani labarin, Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Legas a yau Talata.

A baya, Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jam'iyyar APC a matsayin zababben gwamna.

Kotun har ila yau, ta yi fatali da korafe-korafen 'yan takarar jam'iyyun PDP da LP a zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.