Mu Leka Kotu: Dan Kasuwa Ya Nemi Naira Miliyan 1 Daga Hannun Matarsa Kafin Ya Sake Ta

Mu Leka Kotu: Dan Kasuwa Ya Nemi Naira Miliyan 1 Daga Hannun Matarsa Kafin Ya Sake Ta

  • Wata kotun 'Upper Area' da ke Abuja ta cika da mutane yayin da ake sauraron wata shari'ar miji da mata bai ban mamaki
  • Nasiru Yunusa ya nemi matarsa Aisha Hamisu ta biya shi naira miliyan daya idan har tana so ya sake ta, lamarin da ta ce naira 50,000 kawai za ta biya
  • Tun a watan Afrelu 202 ne ma'auratan suka fara samun matsala a aurensu, inda Nasiru ya kori Aisha daga gidansa ba tare da sawwake mata ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Wani dan kasuwa mai suna Nasiru Yunusa ya yiwa matarsa ​​Aisha Hamisu tayin sakin auren da ba a saba gani ba: ta biya shi naira miliyan daya sannan ta yi tafiyar ta.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai sabon farmaki kauyen Sokoto, sun yi mummunar barna

Ma’auratan, wadanda suka yi aure a karkashin tsarin shari’ar Musulunci a shekarar 2021, kuma iyayen ‘yar watanni 13, suna gaban kotun Upper Area dake Kubwa, FCT, kan neman kashe auren.

Magidanci zai saki matarsa ida ta biya shi naira miliyan daya
Magidanci ya shaida wa wata kotun Abuja cewa zai saki matarsa idan har ta biya shi naira miliyan daya. Hoto: High court
Asali: UGC

Bukatar Nasiru kafin ya saki matarsa

Aisha ce ta shigar da karar inda ta nemi kotu ta raba auren saboda wulakancin da Nasiru ya ke yi mata, inda ta ce ya kore ta da 'yarsu daga gidan shi a watan Afrelu 2022.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai Nasiru ya amince da yin sulhu da matar ma damar za ta biya sa naira miliyan daya da ya kashe kan shari'ar, da kuma wasu kudi da ya kashe a zaman kotun, Leadership ta ruwaito.

Ya ce idan har ta biya kudin to zai ba ta takardar saki, yana mai shaidawa kotun cewa:

"Ina da hujjoji da suka nuna na kashe naira miliyan daya ta dalilinta

Kara karanta wannan

Babban hafsan tsaro CDS ya faɗi halin da ake ciki a bincike kan jefa Bam a taron Musulmai a Kaduna

Aisha ta yi martani kan bukatar mijinta

Amma a nata bayanin, Aisha ta ce sam ba ta da wani sauran muradi na Nasiru, kuma tsawon zamanta a gidan iyayenta bai taba tallafa mata da kudi ba, hatta haihuwar 'yarsu ita ta yi komai.

"Domin kawo karshen aurenmu, zan biya shi naira 50,000 kudin sadakin da ya biya na aure na, amma banda wannan, babu wasu kudi da zan iya ba shi."

A cewar ta game da bukatar Nasiru na biyansa naira miliyan daya.

The Guardian ta ruwaito Mai shari'a Mohammed Wakili ya dage sauraron karar har zuwa ranar 8 ga watan Janairu, inda ake sa ran za a sake kallon wata diramar kan bukatar Nasiru.

Kotu ta yanke hukunci kan matashin da ya cinna wa mahaifiyarsa wuta

Mai shari'a a wata kotun jihar Niger ya ba da umurnin rataye wani matashi da aka kama da laifin kashe mahaifiyarsa ta hanyar cinna mata wuta a jihar.

Kara karanta wannan

Tsaka mai wuya: Sama da 'yan Najeriya 1,000 aka damfara da sunan sama masu aiki a Burtaniya

Shekaru biyu da suka gabata ne matashin mai suna Stephen Jiya ya sheke mahaifiyarsa mai shekaru 61 bisa zarginta da silar bacewar matarsa a Suleja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.