Dalilin da Yasa Yaki da Shugabannin Najeriya Bai da Amfani, Malamin Addini

Dalilin da Yasa Yaki da Shugabannin Najeriya Bai da Amfani, Malamin Addini

  • Fasto Richard Adeboye ya shawarci yan Najeriya da su taya shugabannin kasar da addu'a domin samun sauyin da ake muradi
  • A cewar Adeboye, zanga-zanga da fadace-fadacen da aka yi a baya ba su sa an yi nasara a kan su ba
  • Malamin addinin ya ce ya kamata yan Najeriya su sake kusantar Ubangiji sannan su yi abun da ya kamata ayi a zahiri

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Babban faston cocin RCCG, Fasto Richard Adeboye, ya fada ma yan Najeriya abun da ya kamata su yi wa shugabannin siyasa a kasar.

Adeboye ya ce ya kamata yan Najeriya su taya shugabanni a kasar da addu'a maimakon yin zanga-zanga da tsine masu, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Babban hafsan tsaro CDS ya faɗi halin da ake ciki a bincike kan jefa Bam a taron Musulmai a Kaduna

Fasto Adeboye ya bukaci yan Najeriya da su koma ga Allah
Dalilin da Yasa Yaki da Shugabannin Najeriya Bai da Amfani, Malamin Addini Hoto: Pastor Enoch Adeboye
Asali: Facebook

Ya ce an yi zanga-zanga da fadace-fadace a baya kuma hakan bai haifar da sakamakon da ake muradi ba, Rahoton New Telegraph.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin addinin ya bayyana hakan ne da yake zantawa da namena labarai a wajen taron addu'a na 2023 a makarantar Shimawa High School, jihar Ogun.

Fasto Adeboye ya ce:

“Mu kara kusantar Allah. Sannan mu yi imani da Allah da dduk abin da ya kamata mu yi a zahiri, mu yi shi. Ba wai muna cewa mu yi zanga-zanga ko fada da su gwamnati bane. Mu yi hakan a baya, ba mu cimma nasara a fadan ba.
"Littafi mai tsarki ya bayyana cewa zuciyar sarki na a hannun Ubangiji. Idan da kawai za mu yi magana da Allah cewa ka sa su anan, ina ganin abubuwa za su sauya kuma nan kusa, abubuwa za su inganta."

Kara karanta wannan

Direban tasi ya tsinci jakar kudi a motarsa, bidiyo ya bayyana yayin da ya mayar da shi

Fasto Adeboye ya hango makomar Najeriya

A baya mun ji cewa Enoch Adeboye, shugaban cocin RCCG, ya ayyana cewa makomar Najeriya na da girma duk da tarin kalubale da take fuskanta.

Kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto a ranar Asabar, 16 ga watan Disamba, Fasto Adeboye ya bayyana hakan ne yayin wani taro da aka gudanar a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

An shirya taron ne domin karrama tsohon babban kwamishinan Najeriya a Amurka, Sharafa Tunji-Ishola, rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng