Mahaifin Ministan Buhari Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Ya Na da Shekaru 105 a Duniya

Mahaifin Ministan Buhari Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Ya Na da Shekaru 105 a Duniya

  • Allah ya karbi rayuwar mahaifin tsohon Ministan Wasanni, Solomon Dalung ya na da shekaru 105 a duniya
  • Marigayin mai suna Nimgbak William Fabong Dalung wanda tsohon daraktan lafiya ne ya rasu bayan fama da jinya
  • Dalung ya bayyana haka ne yayin da ya ke shirye-shiryen binne mahaifiyarsa da ta rasu a farkon wannan wata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - Tsohon Ministan Wasanni a Najeriya, Solomon Dalung ya sanar da rasuwar mahaifinsa.

Marigayin mai suna Nimgbak William Fabong Dalung ya rasu ne ya na da shekaru 105 a duniya.

Mahaifin tsohon Ministan Buhari ya riga mu gidan gaskiya
Marigayin ya rasu ne ya na da shekaru 105 a duniya. Hoto: Solomon Dalung.
Asali: Facebook

Yaushe Dalung ya bayyana rasuwar mahaifin nasa?

Dalung ya bayyana haka ne ga wakilin Tribune yayin da ya ke shirye-shiryen binne mahaifiyarsa da ta rasu a farkon wannan wata.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Gwamnan Arewa ya sa labule da babban hafsan tsaro na ƙasa kan muhimmin abu 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon ministan ya ce sun kammala shirye-shiryen binne mahaifiyar tasu mai suna Nalkat Yah Chirram da ta rasu ta na da shekaru 90 a duniya a farkon wannan wata da mu ke ciki.

Ya ce:

"Yayin da mu ke shirye-shiryen binne mahaifyarmu a ranar Asabar 23 ga watan Disamba.
"Na samu mummunan labarin rasuwar mahaifi na Nimgbak William Fabong Dalung da ya rasu ya na da shekaru 90 a jiya Litinin 18 ga watan Disamba."

Wane wasiyya marigayin ya yi wa Dalung?

Ya kara da cewa:

"Lokacin da babanmu ya samu labarin rasuwarta, ya kira ni ya mini jaje, inda ya godemin kan yadda na ke kula da su."

Dalung ya kara da cewa mahaifin nasa ya fada masa cewa ya yi hakuri shi ma ya na kan hanyar tafiya, cewar Intel Region.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Kwankwaso ya kai ziyarar jaje game da harin bam a Kaduna, ya tura muhimmin sako

Kafin rasuwar marigayin shi ne tsohon daraktan lafiya da ma'aikatar kananan hukumomi a jihar Taraba.

Buhari ya na dana sani a yanzu

A wani labarin, tsohon Ministan Wasanni da ci gaban matasa, Solomon Dalung ya ce yanzu haka tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya na dana sanin mulkin da ya yi.

Dalung ya bayyana haka ga manema labarai inda ya ce mukarraban tsohon shugaban kasar su suka jawo masa bakin jini a idon al'ummar kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.