Yan Bindiga Sun Sace Basarake da Babban Limami, Sun Bukaci N5m
- Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyen Rakyabu da ke ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara
- Ƴan bindigan sun kutsa har cikin gida sun yi awon gaba ba da hakimi tare da babban limamin ƙauyen
- Bayan sace mutanen biyu, ƴan bindigan sun nemi da a biya su N5m a matsayin kuɗin fansa kafin su sake su
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Wasu ƴan bindiga sun sace Hakimin ƙauyen Rakyabu da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, Magaji Sa’idu da babban limamin ƙauyen Malam Abdullahi.
Wani mazaunin yankin, Amadu Mohammed ya shaida wa jaridar The Punch cewa ƴan bindigan sun sace hakimin ƙauyen da babban limamin daga gidajensu a daren ranar Lahadi.
Nawa ƴan bindigan suke nema?
A cewar Muhammad, ƴan bindigan sun buƙaci N5m a matsayin kuɗin fansa, inda al’ummar garin suka tara Naira 500,000 ta hanyar karo-karo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya koka da cewa duk da karɓar Naira 500,000 ƴan bindigan sun ƙi sakin hakimin ƙauyen da Limamin, rahoton Daily Post ya tabbatar.
A kalamansa:
"Lokacin da ƴan bindigan suka aike da saƙon neman N5m a matsayin kuɗin fansa, iyalan mutanen biyu da aka sace ba su samu damar haɗa wasu kuɗaɗe ba."
"Don haka ne muka yanke shawarar ƙaddamar da gidauniyar roƙo inda muka samu kuɗi N500,000 muka kai wa ƴan bindigan."
"Sun karɓi kuɗin suka ce mana, dole ne mu biya sauran kuɗaɗen da suka rage wato N4.5m."
Wane kira aka yi ga gwamnati?
Mohammed ya ce tara N4.5m abu ne da ba zai taɓa yiwuwa gare su ba, domin ƴan bindigan sun yi awon gaba da duk wasu dabbobin da za su iya sayar da su domin samun kuɗi.
Ya yi kira ga gwamnatin jihar da jami’an tsaro da su yi wani abu domin ceto hakiminsu da kuma babban Limamin.
Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar ba, ASP Yazid Abubakar, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Ƴan Bindiga Sun Mamaye Wani Gari a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa mutanen garin Zurmi da ke ƙaramar hukumar Zui ta jihar Zurmi na fuskantar hare-haren ƴan bindiga ba ƙaƙƙautawa.
A mako ɗaya yan bindiga sun farmaki garin har sau hudu, inda suka kashe mutum uku da sace wasu 16, tare da ƙona ofishin ƴan sanda da motocin aikin soja guda biyu.
Asali: Legit.ng