Abba Gida Gida Ya Dakatar da Masu Gadin Asibiti Kan Aikata Laifi 1 Tak
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi maganin wasu masu gadin asibiti da suka nuna sakaci a kan aikinsu
- An dakatar da masu gadin ne yayin da wani mutum da matarsa ke nakuda ya isa asibitin amma ya gaza samun martani daga wajensu
- Dr. Mansur Nagoda, sakataren hukumar kula da asibitocin jihar Kano, ya tabbatar da batun dakatar da su a cikin wata sanarwa da ya saki
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta dauki tsatsauran mataki a kan masu gadin adibiti, daga kokacin da take na inganta bangaren lafiya a jihar.
A ranar Litinin, 18 ga watan Disamba ne gwamnatin jihar ta dakatar da masu gadin asibitin mata na Imam Wali da ke jihar.
Makasudin sallamar masu gadin asibitin
An raba masu gadin da aikinsu ne saboda sakacinsu wanda ya yi sanadiyar da wata mai juna biyu ta haifi danta a cikin mota a gaban asibitin, rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babban sakataren hukumar kula da asibitoci na jihar Kano, Dr. Mansur Nagoda, ya tabbatar da dakatar da masu gadin a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Samira Suleiman ta fitar.
A cewar Dr. Nagoda, mijin matar yana ta kwankwasa kofar asibitin amma ba a ga mai gadi ko daya ba wanda hakan yasa mijin daukar bidiyon faruwar lamarin sannan ya yada shi.
A cewar sanarwar:
“Dr. Nagoda ya amince da dakatar da masu hadin asibitin mata na Imam Wali sannan ya umurci yankin da ya samar da sabbin masu gadi tare da tura su wajen nan take.
"Ci gaban na zuwa ne bayan yaduwar bidiyon matar da ke nakuda wacce daga baya ta haihu a cikin mota saboda sakacin da ya faru daga bangaren masu gadin cibiyar."
An gargadi Kotun Koli kan shari'ar Kano
A wani labari na daban, mun ji cewa Eunice Atuejide, yar takarar jam'iyyar Labour Party (LP) na mazabar Apapa a zaben 2023, ta bukaci Kotun Koli da ta yanke hukunci da zai ba Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP nasara.
A wata hira ta musamman da ta yi da Legit Hausa a ranar Asabar, 16 ga watan Disamba, Atuejide ta jaddada cewar ya kamata muradin mutane ya yi tasiri a hukuncin karshe da Kotun Koli za ta yanke kan takaddamar zaben gwamnan jihar Kano.
Asali: Legit.ng