Katsina, Bayelsa da Jihohi 6 Ba Za Su Rayu Idan Babu Kudin Gwamnatin Tarayya ba

Katsina, Bayelsa da Jihohi 6 Ba Za Su Rayu Idan Babu Kudin Gwamnatin Tarayya ba

  • Mafi yawan gwamnoni ba su iya aiwatar da komai ba tare da an raba kudin mai a asusun FAAC ba
  • Gwamnoni suna samun kudi ne ta harajin ma’aikata na PAYE, harajin tituna, da kudi daga ma’aikatu
  • Rahoton da aka fitar na bayanin 2022 ya nuna da kason FAAC kusan duk gwamnoni suka dogara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Rahoton ASVI da ke nuna halin da jihohin Najeriya su ke ciki a duk shekara, ya nuna jihohi da-dama sun dogara ne da FAAC.

Idan aka cire kudin da gwamnatin tarayya ta ke aikowa jihohin kasar, Daily Trust ta ce an gano cewa za a samu matsalar tattalin arziki.

Gwamnoni
Gwamnonin jihohi ba su samun IGR Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

IGR bai kai 10% na FAAC a Jihohi 6 ba

Kara karanta wannan

Babban hafsan tsaro CDS ya faɗi halin da ake ciki a bincike kan jefa Bam a taron Musulmai a Kaduna

Jihohin Bayelsa, Kebbi, Katsina, Akwa Ibom, Taraba da Yobe ba su iya samun isassun kudin da za su iya rike nauyinsu su sai an raba FAAC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton da Economic Confidential ta fitar a garin Abuja ya nuna harajin da gwamnati ke tatsa a jihohin bai kai 10% na kason FAAC ba.

Mafi yawan abin da jihohi su ke samu ba zai isa su yi ko da rabin ayyukansu ba, sun dogara ne da abin da aka raba daga asusun hadaka.

Legas tayi wa sauran jihohi 30 nisa

Jihohi 36 sun samu N1.8tr a matsayin haraji a shekarar 2022, amma idan aka duba za a ga Legas kadai ta tara N651bn daga cikin kudin.

Abin da jihar Legas ta samu ya zarce harajin da jihohi 30 su ka tatsa a shekarar 2022.

Su wane jihohi ke iya samun IGR?

Kara karanta wannan

Duka yarjejeniya 8 da aka dauka wajen sasanta Wike da Gwamna Fubara a Aso Rock

Jaridar ta ce jihohi masu kokari idan aka kamanta harajinsu da kasonsu na FAAC su ne: Legas, Ogun, Ribas, Kaduna, Kwara, Oyo da Edo.

A Arewa, Kaduna, Kwara da Nasarawa ne kurum harajin da su ke samu ya kai akalla 20% na abin da ake ba su daga asusun FAAC a shekara.

Akwa Ibom da Bayelsa ba su samun kudin kirki a karon kansu, sai dai su jira kason danyen mai domin sun fi kowa samun kudi mai tsoka.

Farfado da tattalin arzikin Najeriya

Aisha Rimi ta ce akwai kamfanoni sama da 20 da su ke da niyyar fara kasuwanci a kasar nan kamar yadda aka samu labari a makon jiya.

Wadannan kamfanonin kasashen katare za su taimaka wajen ganin matasa sun samu ayyukan yi sannan gwamnati ta samun kudin shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng