Daga Tambayar Mace 'kin iya kunu?', 'Yan Sanda Sun Cafke Wani Mutum a Jihar Kano

Daga Tambayar Mace 'kin iya kunu?', 'Yan Sanda Sun Cafke Wani Mutum a Jihar Kano

  • An samu wani mutumi da ya addabi wata mata a kan hanya ko ta iya yin kunu a jihar Kano
  • Nan take wannan Baiwar Allah ta shigar da kara a wani ofishin 'yan sanda saboda an dame ta
  • Yanzu mutumin yana hannun jami’a kamar yadda kakakin dakarun ‘yan sanda ya sanar a shafinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Wani mutumi ya shiga hannun ‘yan sandan Najeriya saboda yadda ya matsawa wata mata a hanya.

Kamar yadda Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano ya sanar a Facebook, matar ta shigar da kara a ofishinsu.

'Yan sanda
'Yan sanda sun kama shi a Kano Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa/The Online Cook
Asali: Facebook

DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce matar ta na tafiyarta a gefen titi sai mutumin ya rika bin ta yana addabar ta.

Kara karanta wannan

‘Dan APC ya fadawa Tinubu gaskiyar halin da talaka yake ciki ya nemi a dauki mataki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kin Iya Kunu?

Da ya dame ta da tambayar "Kin Iya Kunu?", ita kuma sai ta shigar da kararsa a ofishin ‘yan sanda da ke kusa.

A sanarwar da ya fitar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce wannan mutumi yana tsare a bayan kantarsu a halin yanzu.

Mai magana da yawun bakin ‘yan sandan ya fadi wannan labari ne domin ya zama darasi ga masu irin wannan hali.

Matar ta iya kunu ko kuwa?

Da wani ya nemi jin ko wannan mata ta iya kunun, sai Abdullahi Kiyawa ya fada masa zai iya zuwa ya bincika.

Gwarzon jami'in tsaron bai fadi matakin da aka dauka ba a kan wannan mutumi.

A cewar kakakin dakarun ‘yan sandan reshen Kano, matar za ta dawo ofishin Anti Daba da ke unguwar Tal’udu.

Baki shi ke wanke wuya

"Ya ga wata Baiwar Allah tana tafiya a gefen titi, ya bita yana ta ce mata, "Kin Iya Kunu", har ya fusata ta, taje ta shigar da korafi a Ofishin 'Ƴan Sanda.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Kwankwaso ya kai ziyarar jaje game da harin bam a Kaduna, ya tura muhimmin sako

Yanzu haka wannan matashin yana tsare a bayan "Counter".
Gani ga wane ..."

- Abdullahi Haruna Kiyawa

Tallafin Abdulmumin Jibrin a Kano

Ana da labari cewa Honarabul Abdulmumin Jibrin ya tallafawa mata 500 a tashi guda a garin Kofa da ya fito a jihar Kano

‘Dan majalisar tarayyan ya rabawa matan mazabarsa kudi domin su iya rike kan su a halin tsadan rayuwar da ake ciki a yau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng