Tsaka Mai Wuya: ’Yan Sanda Sun Cafke Dalibin Jami’ar ATBU da Bindiga, an Tura Shi Sashen CID
Rundunar 'yan sanda ta cafke wani dalibin jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi mai suna Atim Emmanuel kan mallakar bindiga da harsashi
- Kwamishinan 'yan sanda ya bayar da umurnin mayar da Emmanuel sashen SCID don gudanar da binciken sirri da kuma gano ko ya kashe wani da bindigar
- A ranar 11 ga watan Disamba ne rundunar ta samu nasarar kama mai laifin yayin da ya ke fitowa daga makarantar dauke da bindigar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Bauchi - Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta cafke wani dalibin aji uku a jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi mai suna Atim Emmanuel kan mallakar bindiga da harsashi.
Mai magana da yawun rundunar, SP Ahmed Mohammed Wakil ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce an kama dalibin a ranar 11 ga watan Disamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An mayar da Emmanuel sashen SCID don gudanar da binciken sirri
Rundunar ta ce Emmanuel ya dauko bindigar tare da fitowa daga makarantar don fita aikata laifi a cikin gari. Bindigar kirar 'pistol revolver' ce, rahoton Daily Trust.
Wakili ya ce:
"Da aka tuhume shi, Emmanuel ya ce ya karbi hayar bindigar hannun wani Zadog kan naira 12,000. Sai dai ya ce ya mallaki bindigar don kare kansa daga bata gari.
"Kwamishinan 'yan sandan jihar Auwal Mohammed Musa ya ba da umurnin mayar da mai laifin sashin SCID don gudanar da binciken sirri da kuma gano ko ya kashe ko illata wani da bindigar."
Leadership ta ruwaito Wakil na cewa rundunar ta yi kira ga iyaye da shugabanni da su sa ido kan 'yayansu don tabbatar da cewa ba sa yin alaka da abubuwan da ka iya kawo tashin hankali a jihar.
Zainab Dass: Bai kamata JAMB ta kara kudin jarrabawa yanzu ba
Mataimakiyar shugaban daliban jami'o'in birnin tarayya Abuja, Zainab Abdullahi Dass, ta ce bai kamata hukumar zana jarabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ta yi karin kudi yanzu ba.
Idan ba a manta ba a safiyar yau muka ruwaito maku cewa JAMB ta kara kudin zana jarrabawar UTME daga 2024, haka zalika ta fitar da sabbin tsare-tsare na zana jarabawar.
Sai dai wannan karin bai yi wa daliban dadi ba, inda Zainab Dass ta ce 'yan Najeriya na fama da talauci a halin yanzu, karin kudin zai tilasta da yawan dalibai hakura da zuwa manyan makarantu.
Asali: Legit.ng