Kano: Kotu Ta Tsare Matasa 4 Kan Shaye-shaye da Buga Ludo a Cikin Masallaci, Sun Yi Martani

Kano: Kotu Ta Tsare Matasa 4 Kan Shaye-shaye da Buga Ludo a Cikin Masallaci, Sun Yi Martani

  • Dubun wasu matasa ya cika bayan kama su da zargin aikata shaye-shaye a cikin masallaci a jihar Kano
  • Matasan wadanda mazauna Unguwar Rimin Kebe ne da ke Kano har ila yau, sun kware wurin buga wasan ludo a cikin masallaci
  • Wani mai suna Usman Auwalu shi ya kai matasan kara bayan sun yi masa dukan tsiya kan ya yi kokarin hana su harkokinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Kotun Shari'ar Musulunci a jihar Kano ta tsare wasu matasa kan zargin shaye-shaye a cikin masallaci a jihar.

Har ila yau, ana zargin matasan da ke Unguwar Rimin Kebe da buga wasan ludo a masallaci.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Kwankwaso ya kai ziyarar jaje game da harin bam a Kaduna, ya tura muhimmin sako

An tsare matasa 4 kan buga ludo da shaye-shaye a cikin masallacin Kano
Kotu ta gurfanar da matasa 4 kan shaye-shaye da buga ludo a cikin masallaci. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Twitter

Wane hukucin kotun ta yanke a Kano?

Kotun da ke zamanta a unguwar PRP a Gama a karamar hukumar Nasarawa ta gurfanar da matasan ne bayan samun korafi daga wani mai suna Auwalu Usman, cewar AllNews.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Usman ya ce mutanen hudu sun hada baki tare da aikata shaye-shaye da ludo a cikin masallacin tare da yi masa barazana don ya yi musu magana.

Daga bisani matasan sun yi wa Usman dukan tsiya saboda ya musu katsalandan a harkokin rayuwarsu, cewar Daily Trust.

Wane martani wadanda ake zargin su ka yi?

Yayin gabatar da kara, Aliyu Murtala ya karanto tuhume-tuhume kan matasan, daya ne kawai daga cikinsu ya amince da aikata laifin yayin da sauran ukun su ka musanta.

Alkalin kotun, Malam Nura Yusuf ya umarci ci gaba da tsare matasan a gidan gyaran hali har zuwa ranar 3 ga watan Janairun 2024.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya tabbatar da barin Ciyamomi 21 da Kansiloli 239 ofisoshinsu, ya fadi dalili

Har ila yau, ya dage ci gaba da sauraran karar ce don gabatar da shaidu a gaban kotu, cewar Trust Radio.

APC ta musanta zargin yarjejeniya da NNPP

A wani labarin, jami'yyar APC mai mulki a Najeriya ta musanta zargin cewa sun kulla yarjejeniya da takwararta ta NNPP kan bar wa Abba Kabir kujerarshi a Kano.

Jam'iyya ta ce babu inda aka yi wannan zance kuma Shugaba Tinubu ba zai taba amincewa da haka ba saboda shi mai bin doka ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.