Kungiyoyin Kwadago Na NLC da TUC Sun Yi Gargadin Shiga Yajin Aiki Bayan Gwamnatin Tinubu Ta Yi Abu 1
- Ƙungiyoyin ƙwadago sun aika da saƙon gaggawa ga gwamnatin tarayya ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu
- Ƙungiyoyin NLC da TUC sun yi barazanar shiga wani sabon yajin aiki idan gwamnatin tarayya ta yi watsi da alkawuran da ta ɗauka dangane da sabon mafi ƙarancin albashi
- Ƙungiyoyin sun bayyana cewa matakin da gwamnati ta ɗauka na dakatar da biyan albashin N35,000, wani dalili ne da zai sa za ta fara yajin aiki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya na shirin ɗaukar kwakkwaran mataki kan dakatar da biyan albashin ma'aikatan gwamnati, tare da yin gargadi ga gwamnatocin tarayya da na jihohi da su jajirce wajen ƙara mafi ƙarancin albashi daga N30,000 da ake biyan ma'aikata a duk wata.
Gargaɗin yana nuna yuwuwar sake hawa kan teburin sulhu domin tattaunawa game da sabon mafi ƙarancin albashi.
Yayin da Gwamnatin Tarayya ta ware Naira Tiriliyan 1 don gyara mafi ƙarancin albashi a cikin kasafin kuɗinta na 2024, gwamnatocin jihohin dai sun yi shiru kan lamarin, lamarin da ya haifar da fargabar tsadar rayuwa a faɗin ƙasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaushe mafi ƙarancin albashi zai ƙare?
Yayin da ake cigaba da tattaunawa kan sabon mafi karancin albashi, Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa, Idris Mohammed, ya bayyana cewa mafi ƙarancin albashi na N30,000 na yanzu zai ƙare ne a ƙarshen watan Maris ɗin 2024.
Gwamnatin tarayya ta amince da aiwatar da mafi ƙarancin albashi na N30,000 a watan Oktoban 2019 bayan shafe watanni ana tattaunawa.
Sai dai, kuma dakatarwar da aka yi na biyan albashin N35,000 da aka fara yi a baya-bayan nan sakamakon cire tallafin man fetur, ya haifar da damuwa a tsakanin ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC da takwararta ta TUC.
NLC na shirin shiga yajin aiki
Da yake magana game da hakan, mataimakin shugaban TUC, Tommy Etim, ya yi gargaɗin cewa ƙungiyar na iya yanke shawarar fara yajin na tsawon lokaci a taron majalisar zartarwa ta ƙasa na gaba.
A wata hira da jaridar The Punch, wacce aka buga a ranar Lahadi, 17 ga Disamba, Tommy Etim ya ce:
"Sai dai, gwamnati ba ta gayyace mu don ta gaya mana dalilin da ya sa ba su biya ba, don haka muna jira, idan har zuwa ƙarshen watan Disamba ba su biya ba, ina tabbatar muku cewa a taron da za a yi na gaba na NEC, za mu cimma ƙudurin shiga yajin aiki."
Oshiomole Ya Shawarci NLC
A wani labarin kuma, kun ji cewa Oshiomhole ya bukaci ƙungiyoyin kwadago da su tabbatar da biyan albashin ma’aikata a fadin jihohi 36.
Adams Oshiomhole, ya ce ya kamata a biya ma'aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu ƙarin N35,000 don rage tasirin cire tallafin man fetur kafin Kirsimeti.
Asali: Legit.ng