Wani Mutum Ya Fadi Kalaman da Ya Yi Amfani da Su Wajen Sace Zuciyar Matarsa a Twitter
- Wani matashi dan Najeriya ya aika sakon barkwanci ga wata matashiya da ya ci karo da ita a Twitter, yana mai fada mata cewa yana son zai aurenta
- Matashiyar ta ji dadin yanayinsa mai cike da barkwanci sannan ta yarda ta yi hira da shi
- Haduwarsu ba da jimawa ba sai suka gano cewa sun yi tarayya a abubuwa da dama sannan suka fada tarkon soyayya
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Shekaru biyu baya, wani matashi dan Najeriya ya ci karo da shafin wata mata a Twitter kuma nan take kyawunta ya dauki hankalinsa.
Sai ya yanke shawarar aika mata da sako a twitter, amma ba wai kowani irin rubutu ba. Ya so ya sanya ta dariya da kuma jan hankalinta, don haka sai ya aika mata sako mai ban dariya da ke nuna aniyarsa na son aurenta.
Yana ta fatan za ta mayar masa da amsa ba tare da ta share shi ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matashiyar ta cika da mamaki sannan rubutun nasa ya burge ta. Ta ji dadin barkwancin nasa sannan ta yanke shawarar ba shi dama ya shiga rayuwarta.
Ta amsa sakon nasa sannan suka fara hira a tsakaninsu. Bada jimawa ba sai suka gano cewa sun yi kamanceceniya a abubuwa da dama sannan suna jin dadin kasancewarsu tare.
Sun yi musayar lambobin waya sannan suka ci gaba da hirarsu ta wayar tarho. Bayan dan lokaci, sai suka yanke shawarar daukar soyayyarsu zuwa mataki na gaba sannan suka yi aure.
Kalli wallafarsa a kasa:
Masoya sun yi aure bayan shekaru 29
A wani labrin, mun ji cewa wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta garzaya dandalin soshiyal midiya domin yada bidiyon auren iyayenta, wadanda suka shiga daga ciki bayan shekaru 29.
Tuni ma'auratan suka mallaki yara da suka girma a daidai lokacin da suka yi aure a hukumance. Gaba daya abokan yaran sun yi wani sanannen wasa da aka yi na wacece amarya don nunawa duniya ainahin amaryar.
Matashiyar (@misttyceleb1) wacce ta yada bidiyon ta taya iyayenta murna. Mutane da dama sun taya ma'auratan murna, sannan wasu sun yi mamakin dalilinsu na jira na tsawon lokaci.
Asali: Legit.ng