Yan Bindiga Sun Farmaki Manoma a Gona, Sun Halaka Mutum 4

Yan Bindiga Sun Farmaki Manoma a Gona, Sun Halaka Mutum 4

  • Miyagun ƴan bindiga sun kai mummunan farmaki a wasu ƙauyuka biyu na ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Aliyu wanda ya tabbatar da aukuwar harin ya ce ƴan bindigan sun halaka manoma mutum huɗu
  • Kakakin ya kuma bayyana cewa an nemi wasu mutum takwas an rasa biyo bayan harin da ƴan bindigan suka kai

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Ƴan bindiga sun kai farmaki kan manoma a ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Ƴan bindigan a yayin harin da suka kai a ƙauyukan Dantsuntsu da Nahuta a ƙaramar hukumar ta Batsari, sun halaka mutum huɗu, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Sojoji sun halaka yan ta'adda 3 da ceto mutanen da suka sace

Yan bindiga sun halaka manoma a Katsina
Yan bindiga sun halaka mutum hudu a Katsina Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Me ƴan sanda suka ce kan harin?

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Aliyu ya tabbatar da aukuwar harin tare da kisan mutum huɗun da ƴan bindigan suka yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ASP Aliyu wanda ya ce kwamishinan ƴan sandan jihar Katsina na sane da aukuwar lamarin, ya shaida wa manema labarai a wata hira da ya yi cewa wasu manoma takwas sun ɓace.

Wani da ya tsira da ransa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana ta wayar tarho cewa harin na daga cikin wasu da dama a ƙauyukan, lamarin da ya sanya rayuwa cikin wahala ta yadda mutanen yankin suka kasa shiga gonakinsu wajen girbin dankali da sauran amfanin gona.

"Ƴan bindigan sun zo ne yayin da manoman mu ke cikin gonakinsu a ranar Asabar, sai suka kewaye yankin kuma suka fara harbe-harbe daga ko’ina. Wasu sun mutu, wasu sun tsere kuma ba a ga kusan mutum takwas ba." A cewarsa.

Kara karanta wannan

Dalibai mata na jami'ar arewa sun kuɓuta daga hannun yan bindiga, VC ya faɗi halin da suke ciki

Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin ƴan sandan jihar Katsina domin samun ƙarin bayani kan mutanen da ba a gani ba, amma sai dai bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ta waya ba, har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Ƴan Bindiga Sun Halaka Basarake a Taraba

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kashe hakimin garin Sarkin Kudu, Ali Hakimi, da ke ƙaramar hukumar Ibbi ta jihar Taraba. Ƴan bindigan sun kai farmaki ne fadar basaraken.

A cikin ƴan kwanakin baya-bayan nan, tsagerun yan bindigar sun kai hare-hare da dama a fadin masarautar sannan sun yi awon gaba da mutane da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng