Fitaccen Malamin Addini Ya Yi Hasashen Makomar Najeriya Ana Tsaka da Wahala

Fitaccen Malamin Addini Ya Yi Hasashen Makomar Najeriya Ana Tsaka da Wahala

  • Shugaban cocin RCCG, Fasto Enoch Adeboye, ya bayyana cewa shi ya yarda har yanzu Najeriya tana da kyakkyawar makoma
  • Malamin addinin ya bayyana hakan ne a yayin wani taro a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun
  • Adeboye ya bayyana cewa wasu lokutan idan mutne suka yi tunanin Najeriya za ta zama tarihi, sai gano cewa kasar na tsaye da kafafunta

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Abeokuta, jihar Ogun - Enoch Adeboye, shugaban cocin RCCG, ya ayyana cewa makomar Najeriya na da girma duk da tarin kalubale da take fuskanta.

Kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto a ranar Asabar, 16 ga watan Disamba, Fasto Adeboye ya bayyana hakan ne yayin wani taro da aka gudanar a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Manyan malamai sun dira hedkwatar tsaro ta kasa yayin da CDS ya dauki sabon alkawari

Fasto Adeboye ya hango makoma mai kyau tattare da Najeriya
Fitaccen Malamin Addini Ya Yi Hasashen Makomar Najeriya Ana Tsaka da Wahala Hoto: PASTOR E. A. ADEBOYE
Asali: Facebook

Adeboye ya nuna fatan alheri ga makomar Najeriya

An shirya taron ne domin karrama tsohon babban kwamishinan Najeriya a Amurka, Sharafa Tunji-Ishola, rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fasto Adeboye ya ce:

"Najeriya kasa ce ta musamman. Wasu lokutan idan kana tunanin zuwa gobe, Najeriya za ta zama tarihi sai ka tashi washegari sannan ka ga cewa yar yanzu Najeriya na tsaye da kafafunta.
"Koma menene ke faruwa a Najeriya a yau, na yi imani da gaske cewa muna da makoma mai kyau.
"Allah yana da wani ra'ayi na musamman ga al'ummarmu Najeriya kuma ina so ku karfafa gwiwa."

Zan so na mutu ranar Lahadi, Fasto Adeboye

A baya mun ji cewa Fasto Enoch Adejare Adeboye, shugaban cocin RCCG, ya bayyana cewa zai so ya mutu ba tare da damuwa ko rashin lafiya ba.

Kara karanta wannan

Ministan Shugaba Tinubu ya canza jam'iyya a hukumance, ya bayyana dalili 1 tal

Da yake magana a rana ta 3 na wani taron RCCG a dakin taro na cocin da ke jihar Ogun, malamin addinin ya ce zai so ya yi mutuwa irin ta wani kawunsa, wanda ya mutu a bandaki.

A cewar Adeboye, kawunsa ya dawo daga coci a ranar da ya mutu sannan ya ci abincin rana mara nauyi wanda matarsa ta girka yayin da yake jiran a a gama hada masa sakwaran da aka girka masa.

Ya ce sai kawun nasa ya yanke shawarar zuwa bandaki lokacin da matarsa ke kicin tana hada masa sakwaran amma ya mutu a bandakin ba tare da rashin lafiya ko radadi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng