Annobar ‘Korona’ Ta Sake Dawo Wa Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana Kan Lamarin

Annobar ‘Korona’ Ta Sake Dawo Wa Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana Kan Lamarin

  • Jama’a da dama su na ta yada jita-jitar cewa cutar annobar ‘Korona’ ta sake dawo wa Najeriya a ‘yan kwanakin nan
  • Gwamnatin Tarayya ta yi martani kan jita-jitar inda ta bukaci mutane su yi hankali da yada irin wadanan bayanai ba hujja
  • Ministan Lafiya, Dakta Ali Pate shi ya yi martanin bayan da aka yi ta yada jita-jitar cewa cutar ta sake dawo wa Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya ta yi martani kan zargin sake dawowar cutar ‘Korona’ zuwa Najeriya.

Ministan Lafiya, Dakta Ali Pate shi ya yi martanin bayan da aka yi ta yada jita-jitar cewa cutar ta sake dawo wa Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisar dattawa ya yi magana kan rade-radin ya yanke jiki ya fadi a bikin cika shekaru 61

Gwamnatin Tarayya ta yi martani kan bullar cutar 'Korona' a Najeriya
Ministan lafiya ya karyata jita-jitar sake bullar cutar 'Korona'. Hoto: WHO, Ali Pate.
Asali: Facebook

Wane martani FG ta yi kan annobar cutar 'Korona'?

Pate ya yi fatali da labarin inda ya ce babu kamshin gaskiya a cikinsa kuma ya bukaci jama’a su yi watsi da lamarin, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce babu wani binciken kimiyya da ya zai tabbatar da hakan inda ya ce ba wai kawai abu ne da za a yada ba babu bincike.

Ministan ya bayyana haka a wani taro a Otukpo da ke jihar Benue inda ya samu wakilcin hadiminsa, Emmanuel Oduh, Ripples ta tattaro.

Wace hujja FG ta bayar kan annobar cutar 'Korona'?

Ya ce:

"Binciken cutar 'Korona' dole zai zama na kimiyya ne ba abu ne kawai da za a yada haka kawai ba.
"Dole za a iya samun jita-jita amma da zarar an samu bincike ya tabbatar da cewa ba 'Korona' ba ce, to tabbas ba ita ba ce."

Kara karanta wannan

Jigon APC ya bayyana abu 1 tak da zai jawo wa Tinubu faduwa a 2027, ya ba da shawara

Ya ce Najeriya a baya ta yi nasara wurin tabbatar da fatattakar cutar daga fadin kasar baki daya yadda ya kamata.

Majalisa ta bukaci bincike kan kudin tallafin 'Korona'

A wani labarin, Majalisar Wakilai a Najeriya ta bukaci Kwamitin Asusun Gwamnati da ya bincike yadda aka karkatar da kudaden tallafin 'Korona'.

Dan Majalisar daga jihar Adamawa, Nyampa Zakari shi ya bijiro da maganar karkatar da kudaden da aka yi musamman don tallafa wa mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.