Kaddara Ce Ta Kawo Buhari Mulkin Najeriya, Tinubu Ya Magantu Kan Salon Mulkin Tsohon Shugaban Kasar
- Shugaba Tinubu ya taya tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari murnar cika shekaru 81 a duniya
- Tinubu ya bayyana haka ne yayin da ya ke taya tsohon shugaban murnar bikin zagayowar ranar haihuwarsa
- Shugaban ya yaba da irin gaskiya da rikon amana da kuma kishin kasa da tsohon shugaban kasar ya ke da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya taya Buhari murnar bikin ranar zagayowar haihuwarsa a yau Asabar 16 ga watan Disamba.
Tinubu ya yaba da irin gaskiya da rikon amana da kuma kishin kasa da tsohon shugaban kasar ya ke da shi, cewar Premium Times.
An kama wani mutum bayan ya ziyarci surukansa ba tare da sadaki ba, sun dafa abinci da komai na biki
Mene Tinubu ya ce kan Buhari?
Shugaban ya yi wannan magana ne yayin da ya ke taya Buhari murnar cika shekaru 81 in da ya ce Buhari ya kawo ci gaba a kasar wanda ba zai misaltu ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola ya kuma tuna da irin ''bautar a zo a gani da ya yi wa kasa'' a lokulokacin da ya ke mulki a gwamnatin mulkin soja da kuma tsarin dimukradiyya.
Ya ce:
"Buhari ya kasance cikin jajirtattun shugabanni masu rikon amana inda ya sadaukar da rayuwarsa wajen bautar kasa, Buhari ya ja wa kansa dauri a gidan yari duk don kishi da son bauta."
Wane fata Tinubu ya yi wa Buhari?
Ya kara da cewa:
"Samun shugabanni irin aboki na Buhari, na faruwa ne kawai bisa kaddarar Allah, mutum ne mai dattako, idan ya ce zai yi, to zai yi, idan kuma ya ce ba zai yi ba, to ba zai yin ba."
Tinubu ya yi wa tsohon shugaban kasar fatan alkairi da kuma karin shekaru masu albarka.
A karshe, Shugaba Tinubu ya yi masa alkawarin ci gaba da ganin fatansa na son zaman lafiya da ci gaba ba zai gushe ba, cewar Chronicle.
Tinubu ya saka baki a rikicin siyasar Ondo
A wani labarin, Shugaba Tinubu ya sake sanya baki a rikicin siyasar jihar Ondo.
Wannan shi ne karo na biyu da Tinubu ke shiga lamarin rikicin siyasar da ta ki ta ki cinyewa.
Asali: Legit.ng