Tudun Biri: Kwankwaso Ya Kai Ziyarar Jaje Game da Harin Bam a Kaduna, Ya Tura Muhimmin Sako

Tudun Biri: Kwankwaso Ya Kai Ziyarar Jaje Game da Harin Bam a Kaduna, Ya Tura Muhimmin Sako

  • Jigon jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso ya kai ziyarar ta'aziyya game da harin bam a jihar Kaduna
  • Kwankwaso ya bukaci hukumomi su yi kwakkwaran bincike don gano musabbabin wannar matsalar
  • Hadimin sanatan a bangaren yada labarai, Saifullahi Hassan shi ya bayyana haka a shafin X a yau Asabar 16 ga watan Disamba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya kai ziyara jihar Kaduna don jajantawa wadanda harin bam ya rutsa da su a jihar.

Kwankwaso ya kai ziyarar ce a yau Asabar 16 ga watan Disamba inda ya nuna alhininsa kan harin.

Kwankwaso ya kai ziyarar jaje ga wadanda harin bam ya rutsa da su a Kaduna
Kwankwaso ya bukaci yin binciken kwa-kwaf kan harin bam a Kaduna. Hoto: @SaifullahiHon.
Asali: Twitter

Mene Kwankwaso ya ce kan harin bam?

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin sanatan, Saifullah Hassan ya wallafa a shafin X a yau Asabar 16 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Manyan malamai sun dira hedkwatar tsaro ta kasa yayin da CDS ya dauki sabon alkawari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba a manta ba, sojoji sun kai harin bam kan masu Maulidi a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Harin ya yi ajalin mutane fiye da 100 yayin wasu da dama su ka jikkata inda yanzu haka su ke karbar kulawa a asibiti.

Sanatan, yayin ziyarar ya bukaci hukumomi da su dauki mataki kan wannan iftila'i da ya afku, cewar Daily Trust.

Sanatan ya nuna alhininsa kan wannan mummunan hari inda ya yi addu'ar Allah ya jikan wadanda su ka mutu.

Ziyarar gwamnonin Arewa a Kaduna

Harin bam din ya jawo cece-kuce a fadin kasar baki daya inda aka kirayi a hukunta sojojin da ke da alhakin kai harin.

A jiya ma kungiyar gwamnonin Arewa ta kai ziyarar jaje inda ta bada gudunmawar miliyoyin kudade ga wadanda abin ya shafa.

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna Sani ya caccaki kalaman DHQ kan dalilin jefa bam a taron Musulmai, ya nemi abu 1

Har ila yau, Sanatocin Arewacin Najeriya 58 sun kai ziyarar jaje inda su ka ba da gudummawar naira miliyan 58.

Daga bisani sanatocin Majalisar gaba daya sun sadaukar da albashinsu na watan Disamba don kawo sauki ga wadanda abin ya shafa.

Atiku ya tura sakon jaje kan harin bayani

A wani labarin, Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya jajantawa wadanda harin bam ya rutsa da su.

Atiku ya bukaci ayi kwakkwaran bincike don ganin an hukunta wadanda ke da hannu a ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.