An Shiga Jimami Bayan Sarkin Kuwait Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Ya Na da Shekaru 86 a Duniya

An Shiga Jimami Bayan Sarkin Kuwait Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Ya Na da Shekaru 86 a Duniya

  • Allah ya karbi rayuwar Sarkin Kuwait, Sheikh Nawaf Al-Ahmad Al-Sabah ya na da shekaru 86 a duniya
  • Marigayin ya rasu ne a yau Asabar 16 ga watan Disamba kamar yadda masarautar ta tabbatar
  • Wannan na zuwa ne bayan Sheikh Nawaf ya dare kujerar bayan shekaru uku a kan mulki da ke cike da rikici

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Kuwait – Sarkin Kuwait, Sheikh Nawaf Al-Ahmed Al-Sabah ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 86.

Marigayin ya rasu ne a yau Asabar 16 ga watan Disamba kamar yadda masarautar ta tabbatar.

Allah ya karbi Sarkin Kuwait, Sheikh Nawaf a yau Asabar
An Shiga Jimami Bayan Rasuwar Sarkin Kuwait, Sheikh Nawaf. Hoto: Aljazeera.
Asali: Facebook

Yaushe aka sanar da mutuwar Nawaf?

Aljazeera ta tattaro cewa mutuwar marigayin na zuwa ne bayan shekaru uku a kan mulki da ke cike da rikici.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Kwankwaso ya kai ziyarar jaje game da harin bam a Kaduna, ya tura muhimmin sako

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

“Cikin alhini mu na sanar da mutuwar Sheikh Nawaf Al-Ahmad Al-Sabah, sarkin Kuwait.”

A watan Nuwamba, Sheikh Nawaf ya kwanta a gadon asibiti yayin da ya hadu da matsalar rashin lafiya.

Yaushe marigayin ya hau karagar mulki?

Sai dai ba a bayar da cikakken bayani kan rashin lafiyar tashi ba inda daga bisani ya samu lafiya, cewar Arab News.

Sheikh Nawaf ya dare kan kujerar mulki a shekarar 2006 wanda kaninsa Sheikh Al-Sabah Al-Ahmad ya nada shi.

Ya dare karagar mulkin ne bayan rasuwar Sheikh Sabah a watan Satumbar 2020 ya na da shekaru 91.

Yanzu hankula sun karkata ko iyalan sarkin za su zabi mai jini a jiki a matsayin wanda zai gaji kujerar.

Kuwait za ta yi kewar Nawaf saboda kan-kan da kai da ya ke da shi da kuma jajircewa a shugabanci.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Manyan malamai sun dira hedkwatar tsaro ta kasa yayin da CDS ya dauki sabon alkawari

Mahaifiyar Sheikh Haifan ta riga mu gidan gaskiya

A wani labarin, Allah ya karbi rayuwar mahaifiyar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Abdurrazaq Yahaya Haifan a Abuja.

Marigayiyar ta rasu ne da yammacin ranar Juma'a 15 ga watan Disamba Abuja bayan fama da jinya.

Tuni aka yi sallar jana'izarta da misalin karfe 10 na safe a masallacin Zango da ke Gwagwalada da ke birnin Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.