Betta Edu: Matasa Mara Aikin Yi Sun Aike da Sako Mai Muhimmanci Ga Ministan Tinubu

Betta Edu: Matasa Mara Aikin Yi Sun Aike da Sako Mai Muhimmanci Ga Ministan Tinubu

  • Abubuwan da Betta Edu ta yi tun lokacin da ta hau kan karagar mulki a matsayin ministar ayyukan jin ƙai da kawar da talauci an yaba da su
  • An bayyana ta a matsayin mai kawo sauyi da za ta aiwatar da "Ajandar sabunta fata" na Shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Waɗannan kalamai sun fito ne daga bakin gamayyar ƙungiyoyin matasa marasa aikin yi a Najeriya (CUYN) a wani taron manema labarai a Abuja

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Haɗaɗɗiyar ƙungiyar matasa marasa aikin yi a Najeriya (CUYN) ta yabawa ministar harkokin jin kai da yaƙi da fatara, Dr Betta Edu, kan yadda take ba da shawarwarin yin sana’o’i da bunƙasa sana’o’i a tsakanin matasan Najeriya.

Kara karanta wannan

MURIC ta yabi tsohon Shugaba Buhari, ta bayyana yadda ya ceto Najeriya

Ƙungiyar ta yaba da jajircewarta na ganin an gina ƙasa da kuma ƙoƙarin tabbatar da ajandar sabunta fata na Shugaba Bola Tinubu.

An yabi Dr Betta Edu
Dr Betta Edu ta samu yabo kan ayyukan da take yi Hoto: Segun Adeyemi
Asali: Original

A cewar gamayyar, Minista Edu ta nuna jajircewarta wajen ganin ta magance ƙalubalen da matasa marasa aikin yi ke fuskanta a ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin wani taron manema labarai a Abuja a ranar Juma’a, 15 ga watan Disamba, shugaban ƙungiyar Kwamared Adamu Adamu, ya bayyana yadda Edu ke aiwatar da tsare-tsare daban-daban da aka tsara domin ƙarfafa matasa da samar musu da damar samun nasara.

Edu ta cimma nasarori

Adam ya lura cewa Edu ta nuna iyawar jagoranci wanda ya ta'allaƙa kan gaskiya, riƙon amana, da haɗa kai.

Yace:

"Sabon shirin sabunta fata da Dr Betta Edu ke jagoranta ya ba mu mamaki, wannan babban guguwar da ake yi na ajandar sabunta fata ya samar da kyakkyawan fata ga matasa marasa aikin yi a Najeriya."

Kara karanta wannan

Murna yayin da yar bautar kasa ta gina ajujuwa 2 a makarantar da dalibai ke zama a kasa

"Daga shirye-shiryen koyar da sana'o'i zuwa tallafin kasuwanci, waɗannan tsare-tsare sun taka muhimmiyar rawa wajen ba mu kayan aikin da suka dace domin tabbatar da kyakkyawar makoma."

Sun buƙaci Edu da ta ci gaba da bin tsarin da ta ke yi a halin yanzu har sai an samu wani muhimmin ɓangare na matasan ƙasar nan sun kuɓuta daga rashin aikin yi.

FG Ta Faɗi Lokacin Biyan Bashin N-Power

A wani labarin kuma, kun ji cewa, Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na fara biyan bashin watanni tara ga waɗanda suka ci gajiyar shirin N-Power da suka kasance cikin shirin.

Gwamnatin tarayya, ta hanyar National Social Investment Programs (NASIMS), ta ce kwanan nan za a biya bashin N-Power idan an kammala aikin sake fasalin shirin da ake yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng