Tudun Biri: Manyan Malamai Sun Dira Hedkwatar Tsaro ta Kasa Yayin da CDS Ya Dauki Sabon Alkawari
- Babban hafsan tsaro na kasa (CDS), Janar Christopher Gwabin Musa, ya jaddada jajircewarsa na kare kare rayuka da dukiyoyin yan Najeriya
- Ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, 15 ga watan Disamba, yayin da ya karbi bakuncin shugabannin majalisar koli ta shari’a a Najeriya a hedikwatar tsaro
- Malaman Shari'an sun kuma mika goyon bayansu ga Janar Musa, wanda suka yaba da yadda ya tafiyar da lamarin bam da aka jefawa al'ummar Kaduna bisa kuskure
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Shugabannin Majalisar Koli ta Shari’a a Najeriya, karkashin jagorancin Dr Bashir Aliyu Umar, sun ziyarci babban hafsan tsaron kasa (CDS), Janar Christopher Gwabin Musa, a hedikwatar tsaro da ke Abuja a ranar Juma’a, 15 ga watan Disamba.
Nasara: Dakarun sojoji sun tarwatsa mafakar hatsabiban yan bindiga, sun kashe wasu a jihohin arewa 2
A yayin ziyarar, Janar Musa ya bayyanawa majalisar malaman jajircewar rundunar sojin Najeriya don wanzar da zaman lafiya a kasar.
Ya amince da abin takaicin da ya faru a Tudun-Biri a Kaduna, ya kuma tabbatar wa majalisar cewa ya mayar da hankali sosai wajen gudanar da bincike a kan lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Janar Musa ya kuma yi alkawarin aiwatar da mafita mai dorewa domin hana sake afkuwar irin wannan lamari a nan gaba, rahoton The Guardian.
Ya ce:
"Za mu yi duk mai yiwuwa don gano bakin zaren sannan mu tabbatar da ganin hakan bai sake faruwa ba."
Babban hafsan tsaron ya yi karin haske kan matsalolin tsaro da ke addabar kasar, musamman a yankin Arewa maso Yamma.
Ya bukaci shugabanni a matakai daban-daban da su yaki ayyukan ta’addanci ta hanyar yin jagoranci mai kyau da samar da ayyukan ci gaba.
Shugabannin Shari'ar Musulunci sun yabawa CDS Musa
A nasa martanin, Dr Bashir, jagoran tawagar, ya yabawa CDS kan daukar muhimmin tsarin jagoranci wanda ke fifita jin dadin jama'a.
Ya jaddada cewa bai kamata shugabanni su zauna cikin wadata ba yayin da mafi yawan al’ummar kasar ke fama da matsanancin talauci.
Dr Bashir ya lissafa irin sauye-sauye masu kyau da aka samu a tsarin tsaron kasar a karkashin jagorancin babban hafsan tsaro (CDS).
Bugu da kari, ya nuna jin dadinsa kan yadda shugaban tsaron ya jajirce wajen magance lamarin Tudun Biri.
Dr Bashir ya kuma yabawa CDS kan nuna tausayi da kulawa ta gaskiya ga wadanda harin Tudun Biri ya rutsa da su.
Tudun Biri: Za a dau mataki kan sojoji
A gefe guda, mun ji cewa babban hafsan tsaro na kasa, Christopher Musa, ya sha alwashin cewa duk sojan da aka gano yana da laifi a kisan masu Maulidi a Kaduna zai ɗanɗana kuɗarsa.
Ranar 2 ga watan Disamba, jirgin yaƙin sojojin Najeriya ya yi ruwan bama-bamai a taron bikin tunawa da haihuwar Manzon Allah SAW a kauyen Tudun Biri, karamar hukumar Igabi.
Asali: Legit.ng