Babban Hafsan Tsaro CDS Ya Fadi Matakin da Suka Ɗauka Kan Sojoji da Suka Kashe Musulmai a Kaduna

Babban Hafsan Tsaro CDS Ya Fadi Matakin da Suka Ɗauka Kan Sojoji da Suka Kashe Musulmai a Kaduna

  • CDS Christopher Musa ya jaddada cewa duk sojan da aka gano da laifin a harin ɓam ɗin Kaduna zai gane kurensa
  • Babban hafsan hafsoshin tsaron ya ce rundunar soji ba ta ji daɗin kisan da aka yi wa masu Maulidi a kauyen Tudun Biri ba
  • Ya ce kwamitin da za a kafa ya gudanar da bincike zai yi aiki a buɗe kuma ba za a sanya sojoji a ciki ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Babban hafsan tsaro na kasa, Christopher Musa, ya sha alwashin cewa duk sojan da aka gano yana da laifi a kisan masu Maulidi a Kaduna zai ɗanɗana kuɗarsa.

Ranar 2 ga watan Disamba, jirgin yaƙin sojojin Najeriya ya yi ruwan bama-bamai a taron bikin tunawa da haihuwar Manzon Allah SAW a kauyen Tudun Biri, karamar hukumar Igabi.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 19 sun bada tallafi mai tsoka ga Musulman da sojoji suka jefa wa bam a Kaduna

Babban hafsan tsaron Najeriya, Christopher Musa.
Harin Bam a Kaduna: Ba za mu kare duk wani jami'in da aka samu da laifi ba, in ji CDS Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Harin bama-baman, wanda rundunar soji ta ce kuskure ne, ya yi ajalin Musulmai sama da 100 a jihar Kaduna, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tuni dai rundunar sojojin kasa suka ɗauki alhakin kai harin, tana mai cewa dakarun sojin na kan aikin yaƙi da ƴan ta'adda lokacin da suka jefa bam ɗin bisa kuskure.

'Bamu ji daɗin abinda ya faru a Tudun Biri ba'

Da yake magana da manema labarai a Abuja ranar Juma’a, Musa ya ce lamarin abin takaici ne matuka saboda aikin sojojin shi ne kare rayukan fararen hula.

Babban hafsan hafsoshin tsaron ƙasa ya jaddada cewa binciken da za a gudanar kan lamarin zai gudana a buɗe babu ƙunbiya-ƙunbiya.

A rahoton Vanguard, Musa ya ce:

"Lamarin da ya faru a Kaduna abin takaici ne matuka, bai kamata ya faru ba, aikinmu shi ne kare rayukan al'umma, amma ba kisa, raunata ko halaka su ba."

Kara karanta wannan

Zaman Sirri: Abin da Shugaban Hafsun tsaro ya fadawa malamai kan kashe masu Maulidi

“A wancan lokacin, muna cikin zafin rai na bin wasu ‘yan bindiga a yankin, amma abin takaici da rashin sa'a sai hakan ya faru."
“Na yi farin ciki da babban kwamanda ya kafa kwamitin da zai binciki lamarin tare da ba da shawara kan yadda za a kiyaye afkuwar haka nan gaba. Duk abin da ya faru, za mu tantance wadanda suka mutu, mu biya diyya."

Matakin da zamu ɗauka kan sojojin da aka gano da laifi - CDS

CDS Musa ya kara da cewa rundunar soji hukuma ce mai da’a kuma ba za ta kare duk wani jami’in soja da aka samu da laifi a lamarin ba.

"Idan aka same su da laifi tabbas za su fuskanci hukunci kuma ina tabbatar muku da cewa za mu fito fili mu bayyana abinda aka gano. Ko soja ɗaya ba zamu sa a kwamitin binciken ba,” inji shi.

INC ta ɗora laifin rikicin Ribas a wuyan Tinubu

Kara karanta wannan

Peter Obi ya dira Kaduna kan kisan musulmai a bikin Maulidi, ya faɗi matsalar da aka samu tun farko

A wani rahoton na daban Ƙungiyar kabilar Ijaw ta ƙasa (INC) ta ce Bola Tinubu ya yi shiru game da rikicin da ministan Abuja ya tayar a Ribas saboda yana goyon bayansa.

Shugaban INC na kasa, Farfesa Benjamin Okoba, ya bayyana cewa duk wani cin mutunci da aka yi wa Gwamna Fubara ya shafi ƙasar Ijaw.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262