Wike Ya Shiga Matsala Yayin da Ake Zarge Shi Da Aikata Wani Mummunan Laifi
- Rigingimun da suka dabaibaye Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, sun ƙara ɗaukar zafi
- Ana zargin tsohon gwamnan na jihar Rivers cewa ya kitsa kisan wani babban jami'in ƴan sanda
- An kuma tuhumi Wike da wawushe dala miliyan 300 na sake gina yankin Ogoni a jihar Rivers
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - Boma Goodhead, ƴar majalisar wakilai daga jihar Rivers, ta yi iƙirarin cewa Nyesom Wike ne ke da alhakin kitsa kisan Bako Angbashim, DPO na ƙaramar hukumar Ahoada ta Gabas a jihar.
A wani faifan bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta, Goodhead mai wakiltar mazabar Asari-Toru a jihar ta zargi tsohon gwamnan na jihar Rivers da hannu a mutuwar Angbashim.
Ƴar jam’iyyar PDP mai shekaru 53, ta yi kira ga hukumomin tsaro da su binciki Wike tare da tuhumarsa kan lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Juma’a, 8 ga watan Satumba, DPO ɗin ya rasa ransa a wata arangama da wasu ƴan ƙungiyar asiri.
Rundunar ƴan sandan jihar ta kama wasu mutane da suke ganin suna da alhakin kisan, amma Goodhead ta yi iƙirarin cewa Wike ya ɗauki nauyin lamarin.
Ana zargin Wike da wawure dala miliyan 300
Goodhead, ƴar majalisar tarayya kuma ƴar uwar tsohon shugaban tsagerun Neja Delta, Asari Dokubo, ta zargi Wike da yin rashin nasara a rumfar zaɓensa a zaɓen shugaban ƙasa.
Bugu da ƙari, ta yi zargin cewa Wike ya wawure dala miliyan 300 da aka ware domin al'ummar Ogoni, inda ta bayyana ministan na Abuja a matsayin "wanda ya saba da ƙarya kuma mayaudari."
A cewarta, Wike ya yi alfahari da cewa yana da iko da ɓangaren shari’a da fadar shugaban ƙasa.
Fubara Ya Umarci Kwamishinoni Su Yi Murabus
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya umarci dukkan kwamishinonin da ministan Abuja, Nyesom Wike, ya naɗa su miƙa takardun murabus.
Wannan umarnin na zuwa ne daidai lokacin da rikicinsa da magabacin na sa ya ƙara ɗaukar zafi a jihar ta Rivers.
Asali: Legit.ng