Jerin Jami'o'in Addinin Musulunci 5 Da Ya Kamata Ku a Sani a Najeriya Tare Da Bayanai
Akwai Jami'o'in Musulunci da dama da aka kafa a Najeriya da nufin samar da ingantaccen ilimi bisa tsarin addinin musulunci.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jaridar The Nation ta tattaro cewa wadannan jami'o'in suna bai wa ɗalibai ingantaccen ilimi da koyarwar Musulunci.
Manufar kafa irin waɗannan jami'o'in ita ce samar da mahallin da dalibai za su iya koyan darussa iri-iri tare da samun zurfin fahimtar shari'a da dabi'un addinin Musulunci.
Jami'o'in suna taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa ilimin Najeriya kuma suna ba da dama ga masu son yin karatu ta hanyar da ta yi daidai da shari'ar Musulunci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta tattaro muku jami'o'in Musulunci 5 da muke da su a Najeriya, ga su kamar haka:
1. Jami'ar Fountain
Wannan Jami’a mallakin kungiyar Nasrul-Lahi-Il-Fatih Society (NASFAT) ce kuma ita ke kula da harkokin makarantar, tana zama ne a jihar Osun.
Gwamnatin Tarayya ta ba ta lasisin yin aiki a matsayin jami’a mai zaman kanta a ranar 17 ga Mayu, 2007, bisa ga shawarar Hukumar Jami’o’i ta Kasa (NUC).
2. Jami'ar Al-Qalam da ke jihar Katsina
Jami’ar Al-Qalam wadda a da ake kira da jami’ar Katsina, tana kan titin Dutsinma a cikin birnin jihar Katsina da ke Arewa maso Yamma a Najeriya.
An kafa Al-Qalam a shekara ta 2005, kuma ita ce jami'ar Musulunci ta farko mai zaman kanta a Najeriya.
3. Jami'ar Crescent
Fitaccen masanin harkokin shari'a kuma tsohon alkalin kotun ƙasa-da-ƙasa ta Hague, Mai Shari'a Bola Ajibola, shi ne ya kafa jami'ar Crescent da ke Abeokuta a shekarar 2005.
Jami'ar tana daya daga cikin manyan jami'o'in Musulunci a Najeriya kuma an kafa ta a karkashin inuwar kungiyar Islamic Mission for Africa (IMA).
Jami'ar Crescent ta samu lasisi a 2005 bayan amincewar Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar Kula da Jami'o'i ta Kasa (NUC).
4. Jami'ar Al-Hikmah
Gidauniyar Musulunci ta Abdur-Raheem Oladimeji (AROIF) ce ta kafa Jami'ar Al-Hikmah da ke Ilorin a Najeriya a shekara 2005.
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ba wa jami'ar lasisin yin aiki a matsayin jami'a mai zaman kanta a ranar 7 ga Janairu, 2005 (Lasisi mai lamba 010).
5. Jami'ar Summit
Jami’ar Summit, wacce kungiyar Ansar-Ud-Deen Society of Nigeria (ADSN) ta kafa a Offa, tana bayar da ingantaccen ilimi ga daukacin ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da addini, kabila, jinsi ko akida ba, amma bisa tsarin addinin Musulunci.
Jami’ar ta samu lasisin wucin gadi (Jami’a ta 59 mai zaman kanta) wanda NUC ta bata a ranar 5 ga Maris, 2015, kana ta samu Lasisin aiki na dindindin a ranar 1 ga Afrilu, 2019.
Jerin Sunayen Manyan Jami'o'i 20 Mafi Kyau a Duniya
A wani rahoton kuma QS World University Rankings ya wallafa jerin fitattun jami'o'i na sahun gaba a muhallin karatu na shekarar 2024 mai zuwa.
Makarantar fasaha ta Massachusetts, jami'ar Cambridge da jami'ar Oxford ne suka mamaye matsayi ukun farko.
Asali: Legit.ng