Kasafin 2024: Wike Ya Roki Majalisar Tarayya Ta Amince da N17bn da Aka Ware Wa Ma’aikatar FCT

Kasafin 2024: Wike Ya Roki Majalisar Tarayya Ta Amince da N17bn da Aka Ware Wa Ma’aikatar FCT

  • Nyesom Wike, ya roki majalisar dokokin tarayya da ta amince ma'aikatar FCT ta samu naira biliyan 17.2 da aka ware mata a kasafin 2024
  • Ministan Abuja ya bayyana gaban kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattawa da majalisar tarayya a Abuja don kare kasafin ma'aikatarsa
  • A cewar wike, manyan ayyukan da zai yi da kudin sun hada da aikin samar da ruwa, gina cibiyar al'adu da gina husumiyar 'Millennium'

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Ministan babban birnin tarayya (FCT) Abuja, Nyesom Wike, ya bukaci majalisar dokokin tarayya da ta amince da naira biliyan 17 da aka ware wa ma'aikatar FCT daga kasafin kudin 2024.

Wike ya yi wannan roko ne lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattawa da majalisar tarayya a Abuja, a ranar Juma’a, 15 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Harin bam: Gwamnan Kwara ya ziyarci Kaduna, ya ba da tallafin N200m ga iyalan Tudun Biri

Wike ya roki majalisar tarayya ta amince a ba ma'aikatarsa N17.1bn daga kasafin 2024
Wike ya lissafa ayyukan da zai yi idan majalisar tarayya ta amince aka ba ma'aikatarsa naira biliyan 17.1 daga kasafin 2024. Hoto: @GovWike
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa an ware wa ma'aikatar FCT naira biliyan 17.2, inda ya kara da cewa zai yi amfani da kudin wajen karasa wasu muhimman ayyuka da aka fara su aka bari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya fadi ayyukan da zai yi da naira biliyan 17.2

Ministan ya ce naira biliyan biyar an ware ta ne don gudanar da babban aikin samar da ruwa a Abuja, sai naira biliyan 4.5 don tsarawa da gina cibiyar al'adu ta Najeriya da hasumiyar 'Millennium'.

Ya kuma ce an ware naira biliyan uku don gyara sakatariyar tarayya, yayin da aka ware naira biliyan hudu don kammala gidan mataimakin shugaban kasa, The Nation ta ruwaito.

Wike ya kara da cewa an ware naira miliyan 609.7 ne domin samar da matsugunni da ofisoshin kungiyoyin kasa da kasa a FCT.

“Kudin naira biliyan 17.1 ne kawai, don haka me zan iya cewa banda in ce, 'don Allah ku taimaka ku amince da kudin kawai".

Kara karanta wannan

Kasafin 2024: Minista na rokon majalisa ta karawa ma'aikatarsa Naira biliyan 250

A cewar ministan.

Kasafi 2024: Ministan ma'adanai ya nemi karin naira biliyan 250

A wani labarin, ministan bunkasa ma'adanan kasa, Dele Alake, ya ce ma'aikatarsa na bukatar Naira biliyan 250 don hako ma'adanai amma gwamnati ta ware masa Naira biliyan 24.

Mr Alake ya ce dole gwamnati ta zama kan gaba wajen hakar ma'adanai, maimakon kyale kamfanoni suna cin karensu ba babaka a harkar, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.