APC Ta Fadi Zaben 2023 a Jihar Kano Saboda Wani Dalili 1 Tak, Jigon Jam’iyyar Ya Fallasa
- Wani jingon jam'iyyar APC, Abdulsalam Zaura ya dora alhakin faduwa zaben 2023 da jam'iyyar ta yi a jihar Kano kan canja fasalin kudi da aka yi
- A cewar Zaura, canja kudin ana dab da babban zaben kasar, ya jefa 'yan Najeriya cikin mawuyacin hali wanda ya tilasta su juya wa jam'iyyar baya
- Jigon jam'iyyar ya kuma tabbatar da cewa da ace gwamnatin Buhari ba ta canja fasalin kudi ba, da babu abin da zai hana APC cin zabe a Kano
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Abdulsalam Zaura, wani jigon jam'iyyar APC ya yi zargin cewa jam'iyyar su ta fadi zaben 2023 na jihar Kano saboda canja fasalin naira da Shugaba Tinubu ya yi.
Da ya ke jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, Zaura ya ce tsananin wahalar da mutane suka shiga saboda karancin kudi ya sa suka kauracewa jam'iyyar.
Dan takarar sanatan Kano ta tsakiya karkashin APC ya ce ba don canjin kudin ba, da jam'iyyar ta ci kujerar gwamna kuma ta kawo shugaban kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutane sun ki zabar APC saboda bakar azabar da suka sha - AA Zaura
A cewar sa:
"Kasancewar ta jam'iyya mai mulki, dole akwai abubuwan da ba za ka yi wa mutane ba idan kana fuskantar lokutan zabe.
"Misali shi ne canja fasalin naira da CBN ta yi kasa da makonni uku da zabe, munga yadda mutane ke kwana waje don cirar kudi, ko kwana a layin sayen fetur."
AA Zaura ya ce jam'iyyar adawa ta yi amfani da wannan dama wajen kara cusa tsanar APC a zukatan al'umma, wanda kuma ya yi tasiri a zaben 2023, rahoton The Cable.
"A mazabar da na tsaya takara, tsawon shekaru biyu babu wanda ya nuna APC da ya tsaya, kowa na nuna goyon bayansa, amma ana canja kudin, komai ya canja.
A cewar jigon jam'iyyar wanda ya tabbatar da cewa wahala ce ta tilasta jama'a zabar jam'iyar adawa, da tunanin fita daga kangin azabar da suke ciki.
Yadda jami’a ke kashe naira biliyan biyar kan duk wani dalibin likitanci
A wani labarin na daban, kun karanta yadda jami'o'in Najeriya suka yi korafi kan kudaden da su ke samu daga gwamnati da dalibai, wanda a cewarsu ba ya isar su.
A cewar jami'o'in, suna kashe naira biliyan biyar don horas da duk dalibin likitanci guda daya, lamarin da ke zama barazana ga tattalin arzikinsu, Legit Hausa ta ruwaito.
Asali: Legit.ng