Dangote Ya Gwangwaje Dalibai 199 da Tallafin Karatu Don Dogaro da Kansu, Ya Fadi Wasu Shirye-shirye

Dangote Ya Gwangwaje Dalibai 199 da Tallafin Karatu Don Dogaro da Kansu, Ya Fadi Wasu Shirye-shirye

  • Kamfanin Dangote da ke jihar Ogun ya yi abin a yaba bayan ba da tallafin karatu ga 'yan asalin jihar da ke yankin da kamfanin ya ke
  • Har ila yau, kamfanin ya dauki nauyin koya wa matasa sana'o'i daban-daban don ba su jari a karshe saboda dogaro da kansu
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wasu dalibai kan tallafin karatun da kamfanin Dangote ya bai wa dalibai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ogun - Kamfanin Samintin Dangote ya ba da tallafin karatu ga dalibai 119 a jihar Ogun.

Kamfanin ya ba da tallafin ne ga 'yan asalin jihar da ke yankin da kamfanin ke gudanar da harkokinsa.

Kara karanta wannan

Jami'in NSCDC da ya yi suna kan katobarar 'Oga at the Top' ya samu karin girma, an tuna baya

Dangote ya bai wa dalibai 119 tallafin karatu da koya wa matasa sana'o'i
Dangote tallafawa dalibai 119 da kudin tallafin karatu don dogaro da kansu. Hoto: Dangote Group.
Asali: Getty Images

Wane tallafi kamfanin Dangote ya bayar?

Har ila yau, kamfanin ya ba da tallafi ga manoma 60 da kayayyakin bunkasa noma da kuma tallafawa mata 60.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan haka kamfanin ya yi namijin kokari wurin tabbatar da koya wa matasa sana'o'i daban-daban a yankin, cewar Daily Trust.

Daraktan kamfanin, Nawabuddin Azad shi ya bayyana haka yayin wani taro a harabar kamfanin da ke Ibese a jihar Ogun.

Azad ya ce su na inganta rayuwar matasan ne a ko wace shekara don rage zaman banza da kuma dogaro da kansu, cewar Vanguard.

Wane alkawari kamfanin Dangote ya yi?

Ya ce a yanzu haka matasa 30 na karbar horon sana'o'i daban-daban wanda a karshe za a sallame su da kaya don dogaro da kansu.

Ya kuma godewa shugabannin yankin da kuma sauran jama'a kan yadda su ke ba su hadin kai don inganta matasan.

Kara karanta wannan

Kano: EFCC ta gurfanar da daraktan kamfani kan zargin hamdame miliyan 21, an fadi yadda su ka bace

Ya yi alkawarin ci gaba da inganta rayuwar matasan da kuma fadada hakan har zuwa kauyuka 17 da ke yankin.

Legit Hausa ta ji ta bakin wasu dalibai kan wannan lamari:

Yusuf Abubakar, wani dalibi a Jami'ar jihar Gombe ya ce wannan abin a yaba ne sai dai Arewacin Najeriya sun fi bukatar wannan tallafi.

Ya ce a matsayinsa na dan asalin Arewa ya kamata ya tallafa wa daliban yankin da sauran bangarorin rayuwa.

Aminu Muhammad K. shi ma a Jami'ar ya ce babu abin da su ke bukata illa tallafin karatu musamman digiri na biyu.

Ya ce:

"Wannan abin a yaba ne saboda ilimi shi ne ginshikin zaman rayuwa wanda ke kawo ci gaba."

Attajirin Arewa zai gina matatar mai a Najeriya

A wani labarin, bayan Dangote, attajiri a Arewacin Najeriya, Abdussamad Rabiu ya shirya gina sabon matatar mai a jihar Akwa Ibom.

Wannan na zuwa ne bayan Alhaji Aliko Dangote ya kammala gina matatar mai a Najeriya da ake dakon fara aikinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.