Nasara: Dakarun sojoji sun tarwatsa mafakar hatsabiban yan bindiga, sun kashe wasu a jihohin arewa 2

Nasara: Dakarun sojoji sun tarwatsa mafakar hatsabiban yan bindiga, sun kashe wasu a jihohin arewa 2

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar tarwatsa mafakar ƙasurguman 'yan bindiga a jihohin Zamfara da Sokoto
  • Kakakin rundunar Operation Hadarin Daji, Kaftin Yahaya Ibrahim, ya ce sojojin sun halaka yan bindiga biyar, sun kwato makami
  • A cewarsa, dakarun sun kara matsa ƙaimi a yankin da suke da 'yan bindiga a shiyyar Arewa maso Yamma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Dakarun rundunar sojin Operation Hadarin Daji (OPHD) ta samu nasarar lalata mafakar yan bindiga da dama a jihar Zamfara za maƙociyarta jihar Sakkwato.

Rundunar wacce ke aikin tabbatar da zaman lafiya a shiyyar Arewa maso Yamma ta ƙara matsa kaimi a yakin da take yi yayin da ake tunkarar bukukuwan kirsimeti.

Kara karanta wannan

Dakarun sojin Najeriya sun ƙara samun babbar nasara kan ƴan bindiga a jihar Sakkwato

Sojoji sun ragargaji yan bindiga a Zamfara da Sokoto.
Dakarun Soji Sun Ragargaji Maboyar Yan Bindiga a Zamfara da Sakkwato Hoto: Nigerian Army HQ
Asali: Getty Images

A sabbin samamen da suka kai jiya Alhamis, dakarun sojin na haɗin guiwa sun halaka yan bindiga biyar tare da kwato muggan makamai kamar bindigu da alburusai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun rundunar OPHD, Kaftin Yahaya Ibrahim, ne ya tabbatar da wannan nasara a wata sanarwa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Rundunar soji ta fatattaki yan bindiga a Zamfara

Ya ce sojojin sun kai samamen shara a kauyukan Dada, Rukudawa, da Dumburum duk a ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

A cewarsa, yayin wannan samamen, sojoji sun yi musayar wuta da yan bindiga suka nuna musu karfin sanin aiki wanda bisa tilas ƴan ta'addan suka tsere da raunuka.

Ibrahim ya kuma bayyana cewa dakarun sun sheƙe ɗan bindiga ɗaya a musayar wutar da suka yi. A kalamansa ya ce:

Kara karanta wannan

"Zamani ya canza" Shugaban JAMB ya faɗa wa ɗalibai yadda zasu samu aiki bayan gama digiri a Najeriya

"Bugu da ƙari, sojojin ba su tsaya iya nan ba, suka wuce gaba suka tarwatsa mafakar ƙasurguman yan bindiga, Gwaska, Ɗan Karami da Ɗangote, waɗanda suka ari na kare don tsira."
"Da suka bincike wurin, sojojin sun kwato bindigogin Danish guda biyu, Babura biyu, kakin soja guda shida daban-daban, na'urorin sadarwa, da alburusai."

Nasarar da sojojin suka samu a Sokoto

A wani samamen na daban da sojojin rundunar OPHD suka kai a jihar Sakkwato, sun halaka yan bindiga huɗu a kauyen Masasa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

“A yayin arangamar, ‘yan ta’adda da dama sun tsere da raunukan harbin bindiga yayin da sojoji suka kwato bindiga kirar AK-47 daya, Wayar Tecno guda biyu, da kudi N282,050," in ji shi.

Yan bindiga sun shiga Zurmi a Zamfara

A wani rahoton na daban Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 10 yayin da suka kai sabon harin hedkwatar ƙaramar hukumar Zurmi a Zamfara.

Mazauna garin sun bayyana yadda ƴan ta'addan suka shiga garin da yamma, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262