Akpabio Na Cikin Wani Yanayi Bayan Zargin Ya Fadi Yayin Bikin Ranar Haihuwarsa, Bayanai Sun Fito

Akpabio Na Cikin Wani Yanayi Bayan Zargin Ya Fadi Yayin Bikin Ranar Haihuwarsa, Bayanai Sun Fito

  • An shiga rudani bayan shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya fadi a taron bikin zagayowar ranar haihuwarshi
  • Akpabio ya kife ne a jiya Alhamis 14 ga watan Disamba yayin da ake gudanar da bikin a otal din Trascorp Hilton a Abuja
  • Kakakin Majalisar Yemi Adaramodu ya musanta faruwar lamarin bayan wakilin Punch ya tuntube shi kan abin da ya faru

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Shugaban Majalisar Dattawa, Godwill Akpabio ya fadi yayin da ake bikin zagayowar ranar haihuwarsa a Abuja.

Lamarin ya faru ne a jiya Alhamis 14 ga watan Disamba yayin bikin cika shekaru 61 na shugaban Majalisar, Punch ta tattaro.

Kara karanta wannan

Tinubu: Mutum 2 da za su taimakawa gwamnatinmu wajen samun nasara a Najeriya

Akpabio ya fadi a wani taro a Abuja, ya na cikin wani hali
An tabbatar da faduwar tashi a jiya Alhamis a Abuja. Hoto: Godwill Akpabio.
Asali: Facebook

Mene dalilin faduwar Akpabio?

Akpabio bayan bikin ya zauna sai kawai ya fadi kasa a otal din Transcorp Hilton inda aka gudanar da kayataccen bikin, cewar Chronicle.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bikin shi ne karo na biyu da aka gudanar tun bayan fara bikin a ranar 9 ga watan Disamba a birnin Uyo da ke jihar Akwa Ibom.

Kayataccen bikin ya samu halartar manyan baki da taron jama’a wanda aka yi a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo.

Tun farko a yayin bikin an gano shugaban Majalisar ya na magana cikin karfi da gadara ba tare da nuna wata alama ta gajiya ba.

Wata majiya ta bayyana yadda shugaban Majlisar ya kife yayin da ya ke zaune a kujera inda aka dauke shi zuwa asibiti, cewar AllNews.

Mene ake cewa kan faduwar Akpabio?

Kara karanta wannan

"Ainahin dalilin da yasa muka tsige gwamna da yan majalisar PDP 16": Alkalin kotun daukaka kara

Majiyar ta ce:

“Akwai alamun shugaban Majalisar ya galabaita ne, ya na zaune kawai akan kujera sai ya fadi kasa.
“A lokacin ne mutane su ka ankara shugaban Majalisar ya fadi sai aka kwashe shi zuwa asibiti don ba shi kulawa ta musamman.”

Wata majiya ta kara da cewa:

“Bayan Akpabio ya raka shugaban kasa da sauran sanatoci, ya dawo ya zauna kawai sai ya fadi kasa."

Kakakin Majalisar, Yemi Adaramodu ya musanta faruwar lamarin bayan wakilin Punch ya tuntube shi kan abin da ya faru.

Akpabio ya gargadi shugaban EFCC

A wani labarin, shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya gargadi shugaban EFCC kan misali da sunanshi.

Wannan na zuwa ne yayin da Ola Olukoyode ke kiran sunan Akpabio a misalin da ya ke yi a yaki da cin hanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.