Bayan Dangote, Wani Biloniya Dan Arewacin Najeriya Ya Gina Matatan Mai, Kayayyaki Sun Iso Daga China
- Nan bada dadewa ba yan Najeriya za su samu sabon matatan mai, wannan karon a jihar Akwa Ibom
- Ana sa ran kammala aikin matatan man a 2024 kuma an samu karin kayan gini daga China
- Ana sa ran matatan man da za a gina zai rika tace gangan danyen mai 200,000 a duk rana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
Wani jirgin jigilar kayayyaki, dauke da kaya na aikin matatan man fetur na Akwa Ibom, ya isa tashan jirgin ruwa na Calabar da ke Port Harcourt.
Wannan ci gaban dai wani muhimmin mataki ne a aikin gina matatar mai na zamani a jihar Akwa Ibom.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
BusinessDay ta rahoto cewa ana fatan gina matatan man fetur din guda biyu a kananan hukumomin Eket da Onna a jihar.
Biloniyan Najeriya ya gina matatan mai
Kamfanin BUA ne ke daukan nauyin gina daya daga cikin matatan man.
Matatan na BUA za ta rika tace ganga 200,000 na kayayyakin man fetur, ciki har da man Euro-V, man fetur, dizal, man jirgin sama, LPG, da 'polypropylene' don kasuwanin gida Najeriya da kasashen waje.
A cikin wani jawabi da Guardian ta rahoto, Shugaban kamfanin BUA Abdulsamad Rabiu, ya ce idan an kammala, matatan man za ta taimakawa wurin rage dogaro da man da ake shigo da shi daga kasashen waje.
Kalamansa:
"Aikin matatar mai ya yi daidai da hangen nesa na BUA don haɓaka masana'antun cikin gida a muhimman masana'antu inda za mu iya kawo inganci kuma za mu rika
"Da zarar an kammala, wannan katafaren ginin na RFCC zai samar da ingantattun man fetur, dizal, da man jirgin sama da suka dace ƙa'idojin Euro-V na kasuwannin Najeriya da manyan kasuwannin yankuna."
A cewar Oil and Gas Journal, a 2021, Rabiu ya yi alkawarin cewa za a kaddamar da matatan man na Akwa Ibom a 2024.
Matatar Mai Ta Dangote Za Ta Fara Aiki a 2022
A wani rahoton daban kun ji cewa Aliko Dangote mai kamfanin Dangote ya ce matatar mansa za ta fara tace danyen mai a watanni uku na kusa da karshen shekarar 2022.
Mujallar Bloomberg ta rahoto cewa hamshakin dan kasuwar ya ce an yi aikin injina a matatar, sannan 'muna sa ran kafin karshen kwata na uku za mu kasance a kasuwa.'
Dangote ya furta hakan ne yayin da ya yi wata ganawa da manema labarai a wurin aikin gina matatar man da ake yi a Legas.
Asali: Legit.ng