Kano: Ya Kamata Tinubu Ya Roke Su, Shehu Sani Ya Yi Martani Kan Shirin ‘Shoprite’ Na Barin Jihar

Kano: Ya Kamata Tinubu Ya Roke Su, Shehu Sani Ya Yi Martani Kan Shirin ‘Shoprite’ Na Barin Jihar

  • Yayin da kamfanin ‘Shoprite’ a jihar Kano ke shirin barin aiki a jihar, Sanata Shehu Sani ya tura sako ga Shugaba Tinubu kan lamarin
  • Sanatan wanda ya wakilci Kaduna ta Tsakiya ya bukaci Tinubu da ya roke su saboda barinsu jihar zai shafi mutane da dama
  • Sani ya bayyana haka ne a shafinsa na X a yau Alhamis 14 ga watan Disamba bayan samun rahoton cewa kamfanin zai bar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna – Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya tura muhimmin sako ga Shugaba Tinubu kan ‘Shoprite’ a Kano.

Wannan kiran na sanatan na zuwa ne yayin da kamfanin ya shirya barin aiki a jihar Kano, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya nada tsohon soja a matsayin shugaban hukumar Hisbah, ya fadi dalili

Shehu ya tura muhimmin sako ga Tinubu kan shirin 'Shoprite' na barin Kano
Shehu Sani ya bukaci Tinubu ya 'Shoprite' a Kano. Hoto: @Imranmuhdz, @ShehuSani, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Mene Shehu Sani ke cewa kan ‘Shoprite’ a Kano?

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da sanatan ya wallafa a shafin X inda ya bukaci Tinubu da ya roke su kada su bar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehu ya ce idan kamfanin ya bar jihar tabbas zai shafi al’umma da dama da kuma tattalin arzikin jihar baki daya.

Ya rubuta kamar haka:

“Na karanta wata sanarwa cewa ‘Shoprite’ za su bar aiki gaba daya, ya kamata shugaban kasa ya roke su don su tsaya.”

Mene dalilin ‘Shoprite’ na barin Kano?

A cikin wata sanarwa, Kamfanin ‘Shoprite’ ya sanar da barin aiki a reshensu na jihar Kano daga ranar 14 ga watan Janairu.

Kamfanin ya sanar da haka ne a cikin wata sanarwa a yau Alhamis 14 ga watan Disamba a Kano.

Ana hasashen kamfanin zai bar Kano ne saboda matsalar cinikayya da kuma halin tattalin arzikin kasar baki daya.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya bayyana abu 1 tak da zai jawo wa Tinubu faduwa a 2027, ya ba da shawara

Shehu Sani ya fada wa Melaye kotun da zai je

A wani labarin, Sanata Shehu Sani ya shawarci Dino Melaye wane kotu ya kamata ya je shi.

Sani ya ce ya kamata Dino ya je kotun wasan Tennis tun da ya rasa nasara a kotunan Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan dan takarar gwamnan PDP a jihar Kogi ya yi korafi kan zaben da aka gudanar bayan ya kasance na uku a zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.