Harin Bam: Gwamnan Kwara Ya Ziyarci Kaduna, Ya Ba da Tallafin N200m Ga Iyalan Tudun Biri

Harin Bam: Gwamnan Kwara Ya Ziyarci Kaduna, Ya Ba da Tallafin N200m Ga Iyalan Tudun Biri

  • Gwamna AbdulRazaq na jihar Kwara ya ziyarci jihar Kaduna don yin ta'aziyyar mutanen da suka mutu a harin bam din soji a garin Tudun Biri
  • A yayin ziyarar ne gwamnan ya sanar da ba da tallafin Naira miliyan 200 ga al'ummar da wannan waki'a ta shafa
  • A cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar Kwara ta fitar a ranar Alhamis, gwamnan ya nuna jin dadinsa kan dattakon da aka nuna bayan harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kwara - Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya kai ziyarar ta'aziyya ga takwaransa na jihar Kaduna, Uba Sani, tare da ba da tallafin Naira miliyan 200 ga al'ummar Tudun Biri.

Kara karanta wannan

"Ka siyar ka rasa kujerar ka": Gwamnatin Kebbi ta gwangwaje kwamishinoni da motocin alfarma

Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Alhamis, 14 ga watan Disamba.

Gwamnatin jihar Kwara ta ba al'ummar Tudun Biri tallafin N200m
Gwamna AbdulRazaq na jihar Kwara ya ba al'ummar Tudun Biri da ke jihar Kaduna tallafin Naira miliyan 200. Hoto: @followKWSG
Asali: Twitter

Gwamna AbdulRazak ya jinjinawa Uba Sani

A cewar AbdulRazaq, ba za su yi kasa a guiwa ba wajen tabbatar da an yi bincike kan yadda sojoji suka jefa bam ga al'ummar garin da ya yi ajalin sama da mutum 100, The Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"Ina mika sakon ta'aziyya ga gwamnan jihar Kaduna, kungiyar gwamnoni da al'ummar jihar baki daya kan wannan waki'a.
"Ina jinjina wa Gwamna Uba, rundunar soji da shugabannnin al'ummar Kaduna kan dattakon da suka nuna bayan faruwar wannan mummunar waki'ar."

Duba sanarwar a kasa:

Sheikh Bello Yabo ya caccaki Tinubu kan harin Tudun Biri

A wani labarin, babban malamin addini na jihar Sokoto, Sheikh Bello Yabo, ya ce ba harin garin Tudun Biri ne na farko da sojoji suka zubar da jinin 'yan Arewa ba.

Kara karanta wannan

Harin bam a Kaduna: Mazauna garin Tudun Biri sun karyata kai karar gwamnatin Tinubu kotu

A cewar Sheikh Yabo, Najeriya ta fada mugun hannu a mulkin Tinubu, wanda bai damu da tsaron rayukan 'yan Arewa ba, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Malamin addinin ya kuma nuna damuwa kan yadda gwamnati ke ci gaba da tsare Mamu wanda a cewarsa "laifinsa kawai shiga tsakanin masu garkuwa da iyalan wadanda aka sace a jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja".

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.