Bankin Duniya Sun Gaskata Abin da Sanusi II Ya Fada a Game da Kamfanin NNPCL

Bankin Duniya Sun Gaskata Abin da Sanusi II Ya Fada a Game da Kamfanin NNPCL

  • Bankin duniya bai gamsu da yadda kamfanin NNPCL yake aiki ba, yana zargin ba a fadan gaskiya
  • Masanan da ake ji da su sun tattauna a game da tattalin arzikin Najeriya har sun fitar da rahoto
  • Ana yawan zargin NNPCL da boye gaskiyar cinikinsu da abin da ake samu bayan cire tallafin mai

Abuja - Bankin duniya yana zargin cewa kamfanin NNPCL bai fadan gaskiya a game da cinikin da yake yi da kuma tsarin tallafin fetur.

Rahoton NDA na shekarar 2023 ya nuna bankin duniyan yana ganin akwai alamar tambaya a yadda NNPCL ke gudanar da ayyukansa.

Muhammadu Sanusi II
Muhammadu Sanusi II ya soki NNPCL Hoto: @MSII_dynasty
Asali: Twitter

Masanan duniyan sun zargi kamfanin man na Najeriya da cigaba da biyan tallafn man fetur duk da Bola Tinubu ya ce an soke tsarin.

Za a binciki NNPCL a Najeriya?

Kara karanta wannan

Idan aka halatta shigo da shinkafa, siminti da sauransu, farashinsu zai sauko – Bankin duniya

Wani labari da aka samu daga This Day ya ce Ministan tattalin arziki, Wale Edun, a ce gwamnati za ta binciki kudin da ke shiga NNPCL.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da bankin duniyan yake so shi ne jama’a su san gaskiyar abin da ke faruwa game da kudin da ake samu wajen saida man fetur.

Muhammadu Sanusi II ya nemi karin bayani daga NNPCL a kan dalolin da ake samu.

Baya ga haka, bankin yana neman karin bayani kan ribar da aka ci bayan cire tallafin fetur duk da cewa a zahiri yake kudin shiga sun karu.

NNPCL sun boye farashin fetur?

Daga cikin abin da ya sa bankin duniyan ya ce babu gaskiya a aikin NNPCL shi ne ganin yadda farashin fetur ya ki canzawa tun a Agusta.

Farashi ya canza a kasuwannin duniya, amma hakan bai shafi kudin lita a gidajen mai ba, hakan ya sa ake zargin ana biyan tallafin fetur.

Kara karanta wannan

Bankin duniya ya fasa kwai, ya fadi farashin da ya kamata a saida fetur a gidajen Mai

Cibiyar Bretton Woods ta ce ana kashe N380bn a kan tallafin fetur a kowane wata maimakon kudin su shiga baitul-malin gwamnatin kasa.

..."An huta tallafin fetur" - Edun

Punch ta rahoto Wale Edun yana kan bakarsa, yake cewa gwamnati ta samu karin kudin shiga a sakamakon daina biyan tallafin fetur da aka yi.

Edun yace ba don matakin da aka dauka ba, da abubuwa sun sukurkucewa gwamnati, amma duk da haka yace ana fama da biyan bashi.

Ya kamata fetur ya koma N750

A makon nan aka samu labari cewa Bankin duniya ya raina tsadar mai, yace ana saida fetur a farashin da ya yi araha sosai a Najeriya.

Alex Sienaert yace kudin fetur bai yi daidai da farashin kasuwa ba, hakan ya sa ake tunani gwamnatin tarayya ta dawo da biyan tallafi ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng