IPPIS: Shugaba Tinubu Ya Sauya Matakin da Buhari Ya Ɗauka Kan jami'o'i da Wasu Manyan Makarantu

IPPIS: Shugaba Tinubu Ya Sauya Matakin da Buhari Ya Ɗauka Kan jami'o'i da Wasu Manyan Makarantu

  • Majalisar zartarwan tarayya (FEC) ta amince da cire jami'o'in Najeriya da sauran manyan makarantu daga tsarin IPPIS
  • Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan gama taron FEC wanda Bola Tinubu ya jagoranta a Abuja
  • Gwamnatin Muhammadu Buhari ta sha fama da ƙungiyar ASUU kan tsarin biyan ma'aikata albashi wanda aka fi sani da IPPIS

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarƙashin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta cire manyan makarantun gaba da sakandire daga tsarin biyan ma'aikata albashi (IPPIS).

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
FEC ta cire jami'o'in Najeriya, kwalejin fasaha da wasu makarantu daga tsarin IPPIS Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ce ta amince da cire jami'o'in tarayya, kwalejojin fasaha da na ilimi da sauran manyan makarantu daga tsarin IPPIS.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta kitsa rikicin Wike da Gwamna Fubara? Gaskiya ta bayyana

Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman, shi ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan kammala taron FEC wanda Shugaba Tinubu ya jagoranta a fadar shugaban ƙasa ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Tinubu ta canza matakin Buhari

Ya ƙara da cewa a yanzu shugabannin manyan makarantu sun samu sauƙin ɗaukar ma'aikata ba tare da neman izinin shugaban ma'aikatan tarayya ba, Daily Trust ta rahoto.

A cewar Ministan, shugaban ƙasa ya bada umarnin cire dukkan mataimakan shugaban jami'o'i (VCs) daga tsarin IPPIS wanda ya sa ɗaukar ma'aikata ya zama abu mai wahala.

Farfesa Mamman ya ce:

"A taƙaice, shugaban ƙasa da mambobin FEC sun damu ne kawai game da ingancin gudanar da jami'o'i don haka ba shi da alaƙa da batun gaskiya ko wani abu daban."
"Shugaban ƙasa ya gaza fahimtar dalilin da ya sa dole VC na kowace jami'a sai ya bar wurin aikinsa ya garzayo Abuja domin kawai a sanya ma'aikatan da ya ɗauka aiki a IPPIS."

Kara karanta wannan

Rikici ya ƙara tsanani, 'yar majalisa ta yi amai ta lashe, ta sauya sheƙa daga APC zuwa PDP

"Abun dubawa anan shi ne ana tafiyar da jami'o'i ne bisa tanadin doka kuma dokokin sun ba su damar cin gashin kansu a ɓangarori da dama, IPPIS kuma ya toshe musu damar cin gashin kansu."

Da yake tsokaci kan batun, ministan yaɗa labarai, Muhammed Idris, ya ce a yanzu jami'o'i da sauran manyan makarantu sun tsira daga batun tsarin IPPIS.

Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Sabbin Shugabannin ICPC da FCCS

A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da sabon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (ICPC), Musa Adamu a Aso Villa ranar Laraba.

Bayan haka shugaban ya kuma baiwa sabon shugaban hukumar ma'aikata (FCSC) da mambobin hukumar 11 rantsuwar kama aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262