Gobara Ta Lakume Kadarorin Miliyoyin Naira a Wasu Shaguna a Jihar Kwara

Gobara Ta Lakume Kadarorin Miliyoyin Naira a Wasu Shaguna a Jihar Kwara

  • An samu tashin gobara a rukunin wasu shaguna a jihar Kwara inda ta lalata dukiya mai tarin yawa
  • Gobarar ta tashi ne a wurare biyu daban-daban a yankin Tanke na ƙaramar hukumar Ilorin ta Kudu a jihar
  • Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce jami'an hukumar sun samu nasarar kashe gobarar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kwara - Aƙalla shaguna 14 suka ƙone a wata gobara daban-daban sau biyu a yankin Tanke na ƙaramar hukumar Ilorin ta Kudu a jihar Kwara.

Gobarar wacce ta tashi daban-daban ta auku ne a tsakanin yammacin ranar Talata da safiyar ranar Laraba, cewar rahoton The Punch.

Gobara ta lakume shaguna a Kwara
Gobara ta lakume shaguna 14 a jihar Kwara (ba inda lamarin ya auku ba) Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Da misalin ƙarfe 6:00 na yamma a ranar Talata, shaguna bakwai da ke Zion Overcomer, kusa da gidan Duro Suleiman, a hanyar University Road, Tanke, suka ƙone.

Kara karanta wannan

Gobara ta babbake ofisoshi akalla 17 a sakateriyar ƙaramar hukuma 1 a jihar Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gobarar ta biyu ta auku ne a yankin Tanke Oke-Odo kan hanyar University Road da misalin ƙarfe 1:30 na safiyar ranar Laraba, inda wasu shagunan guda bakwai suka ƙone.

Me hukumomi suka ce kan gobarar?

A yayin da take tabbatar da faruwar lamarin, hukumar kashe gobara ta jihar Kwara ta ce jami’anta sun kai ɗauki kan tashin gobarar guda biyu a wurare daban-daban a yankin Tanke inda suka ceto shaguna 16 daga cikin 31 da gobarar ta kama.

Jaridar Leadership ta ce kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Mista Hassan Adekunle, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"An kammala aikin kashe gobarar da misalin ƙarfe 6:11. Daga cikin shaguna 17 da ke cikin ginin, gobara ta shafi bakwai daga cikin shagunan, an tafka asasar N19.3m yayin da kayayyakin da aka ceto sun kai N79.5m."

Kara karanta wannan

Hukuncin tsige Gwamna Abba: Yan sanda sun gurfanar da masu zanga-zanga a gaban kotu

"Sai dai, ba a samu asarar rai ko rauni ba."

Wata gobarar ta sake tashi

Sanarwar ta ƙara da cewa:

"A safiyar ranar Laraba, 13 ga watan Disamban 2023, da misalin ƙarfe 1:30 hukumar kiyaye gobara ta jihar Kwara ta kai ɗauki kan wata gobara a titin University Road a unguwar Tanke Oke-Odo a ƙaramar hukumar Ilorin ta Kudu."
"Bayan sun isa wurin, jami'an mu sun samu nasarar kashe gobarar da ta kama shaguna 16 inda ta ƙona shaguna bakwai."

Hukumar kiyaye gobarar ta ɗora alhakin tashin gobarar guda biyu kan tartsatsin wutar lantarki a wuraren.

Gobara Ta Tashi a Ofishin Zulum

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu tashin gobara a ofishin gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum.

An tattaro cewa gwamnan na a daya ofishinsa da ke sakatariyar Musa Usman lokacin da lamarin ya afku da misalin karfe 12:29 na rana a ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng