Hukuncin Tsige Gwamna Abba: Yan Sanda Sun Gurfanar da Masu Zanga-Zanga a Gaban Kotu
- Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da cewa mutum bakwai da ta cafke kan zanga-zanga, ta gurfanar da su a gaban kotu
- Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa ya ce an gurfanar da su ne a wata kotun majistare da ke Ungogo
- Sai dai, kakakin bai yi ƙarin bayani ba kan.lokacin da aka gurfanar da su ko halin da ake ciki a shari'ar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta gurfanar da wasu mutum bakwai da ake zargi da hannu a zanga-zangar da ta ɓarke a birnin Kano, biyo bayan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na tsige gwamna Abba Yusuf.
An dai kama waɗanda ake zargin ne a ranar 22 ga watan Nuwamba a kewayen Kano Line yayin da suke kan hanyar zuwa gidan gwamnati.
Harin bam kan masu maulidi: Iyalan mutanen da suka rasa ransu sun maka FG kara a kotu, sun fadi bukatunsu
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sanda jihar Kano, Abdullahi Haruna, ne ya bayyana batun gurfanar da su a lokacin da aka tuntube shi domin jin ƙarin bayani kan lamarin a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata hira da jaridar The Punch ta wayar tarho a ranar Talata, Haruna ya ce an gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban babbar kotun majistare da ke Ungoggo a ƙaramar hukumar Ungoggo.
Sai dai, kakakin ya ƙi yin ƙarin bayani, ciki har da kan lokacin da aka gabatar da ƙarar.
Me NNPP ta ce kan lamarin?
Da aka tuntubi shugaban jam’iyyar New Nigeria People’s Party reshen jihar Kano, Alhaji Hashimu Dungurawa, ya ce ba zai iya cewa komai ba game da gurfanar da mutanen waɗanda magoya bayan jam’iyya mai mulki ne a jihar.
"Kamar yadda kuka sani, batun kotu ne, domin haka, ba zan ce uffan ba a kan lamarin a yanzu." A cewar Dungurawa.
Wasu matasa da ake zargin magoya bayan jam’iyyar NNPP ne a ranar 22 ga watan Nuwamba, sun fito kan tituna suna zanga-zangar nuna adawa da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ta kori Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Amnesty Ta Fusata Kan Cafke Masu Zanga-Zanga a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar rajin kare haƙƙin Bil Adama ta duniya, Amnesty International, ta yi magana kan caraf da masu zanga-zanga da ƴan sanda suka yi a Kano.
Ƙungiyar ta yi tir da matakin da ƴan sandan suka ɗauka na cafke mutanen da suka fito nuna adawarsu kan hukuncin tsige Gwamna Abba.
Asali: Legit.ng