Daga Ƙarshe FG Ta Bayyana Masu Daukar Nauyin Ta'addanci da Hako Ma'adanai Ba Bisa Ka'ida Ba

Daga Ƙarshe FG Ta Bayyana Masu Daukar Nauyin Ta'addanci da Hako Ma'adanai Ba Bisa Ka'ida Ba

  • Ministan ma’adanai, Dele Alake, ya yi ikirarin cewa wasu ƴan Najeriya masu haƙo ma’adinai ba bisa ka’ida ba ke ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci a ƙasar nan
  • Alake ya bayyana haka ne a lokacin da ya bayyana gaban ƴan majalisa domin kare kasafin kudin shekarar 2024 na ma’aikatarsa a Abuja
  • Alake ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki a ƙasar nan da su mai da hankali sosai kan harkar haƙar ma’adanai da ya ce tana iya samarwa ƙasar nan tiriliyan ɗaya a duk shekara

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Dele Alake, ministan ma'adinai, ya yi zargin cewa "manyan ƴan Najeriya" da ke da hannu wajen haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba, suna ɗaukar nauyin ta'addanci da ƴan bindiga a ƙasar nan

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun halaka sojoji 4 a wani sabon hari, bayanai sun fito

Kamar yadda jaridar ThisDay ta ruwaito, Alake ya bayyana cewa galibin masu hakar ma’adanan ba bisa ƙa'ida ba, ba ƴan kasashen waje ba ne.

FG ta fadi masu daukar nauyin ta'addanci a Najeriya
Alake ya zargi manyan yan Najeriya da daukar nauyin ta'addanci Hoto: @AlakeDele
Asali: Twitter

Ya ƙara da cewa abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda akasarin ƴan ƙasashen ƙetare da suke gudanar da ayyukan hakar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a kasar nan, ba su da cikakkun takardun shaidar shigowa ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alake ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 12 ga watan Disamba a Abuja lokacin da ya bayyana gaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da ma’adanai domin kare kasafin kuɗin 2024, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Su waye ke ɗaukar nauyin ta'addanci?

Kalamansa:

"Ƴan Najeriya ne manyan mutanen da ke ɗaure musu gindi. Muna gano su ta hanyar amfani da ƙarfi da dabara. Mun ƙarfafa gwiwar ƴan ƙananan masu haƙar ma'danai ba bisa ƙa'ida su kafa kamfanoni."

Kara karanta wannan

Kungiyar TUC ta aike da muhimmin gargadi ga Shugaba Tinubu kan karin albashin N35,000

Da yake cigaba da bayani, ministan ya bayyana cewa domin haƙar ma'adanai ya samar da kuɗaɗen shigar da ake buƙata, akwai buƙatar samar da babban kamfani wanda ƴan ƙasashen wajen za su yi hulɗa da shi, kamar irin kamfanin NNPCL.

Ya bayyana Naira biliyan 29 da aka ware wa ma’aikatar a matsayin kasafin kudinta na shekarar 2024 a matsayin wanda ya yi kaɗan, ya kuma nemi taimakon ƴan majalisar don ganin an samar da isassun kuɗaɗe a fannin.

Muna Dab da Bankwana da Rashin Tsaro, Badaru

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan tsaro, Najeriya, Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana cewa Najeriya na daf da bankwana da rashin tsaro da ya daɗe yana ci mata tuwo a ƙwarya.

Ministan ya ce idan gwamnati ta samar da kayan aiki na zamani ga jami'an tsaro to ba shakka an kawo karshen rashin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng