Shari’ar Gwamnan Kano: Lauya Ya Yi Hasashen Makomar APC, NNPP a Kotun Koli

Shari’ar Gwamnan Kano: Lauya Ya Yi Hasashen Makomar APC, NNPP a Kotun Koli

  • Akwai kaddarar da ke jiran Gwamna Yusuf na jihar Kano a Kotun Koli kan karar da ya shigar na kalubalantar korarsa da Kotun Daukaka Kara ta yi
  • Wani lauya, Ismail Balogun ya ce akwai abin zargi a hukuncin Kotun Daukaka Karara, sai dai da wuya Kotin Koli ta kori hukunci iri daya da kotuna biyu suka yanke
  • Kotun Daukaka Kara da kotun kararrakin zabe sun kori Yusuf daga gwamnan Kano tare da ayyana Gawuna matsayin wanda ya lashe zaben 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Tun bayan da Kotun Daukaka Kara mai zama a Abuja ta kori Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, ake ta hasashen abin da ka iya faruwa a Kotun Koli kan shari'ar jihar.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta yanke hukuncin karshe kan shari'ar Sanatan PDP, ta ci tarar dan takara

Kotun Daukaka Kara ta kori gwamnan kan cewar ba shi da shaidar zama dan jam'iyyar NNPP, lamarin da wani lauya Ismail Balogun ke kallo matsayin "abin zargi".

Abba Kabir Yusuf/Nasir Yusuf Gawuna/Gwamnan Kano
Lauya ya yi hasashen makomar Gwamna Abba Yusuf da Nasir Gawuna a Kotun Koli. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Nasir Yusuf Gawuna
Asali: Twitter

A zantawarsa da Legit Hausa, Balogun ya yi nuni da cewa yakan yi wahala Kotun Koli ta kori hukunci iri daya da kananan kotuna suka yanke, sai da babban dalili.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ya sa kotun kararrakin zabe ta kori Gwamna Yusuf na Kano?

Kafin Kotun Daukaka Kara ta kore shi, kotun kararrakin zabe ce ta fara korar Gwamna Yusuf bayan cire kuri'u 165,663 daga na Yusuf, bisa zargin ba su da sitamfi da kwanan wata.

Kotun ta umurci INEC ta ayyaha Nasir Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC matsayin wanda ya lashe zaben tare da ba shi takardar shaidar hakan, Legit ta ruwaito.

Lauya ya yi hasashen makomar Gwamna Abba a Kotun Koli

Kara karanta wannan

Kotun Koli: Fitaccen malamin addini ya yi sabon hasashe kan takaddamar zaben Kano

Da ya ke martani kan hukuncin Kotun Daukaka Kara da na kotun kararrakin zabe, babban lauyan ya ce akwai kaddarar da ke jiran gwamnan NNPP a Kotun Koli.

Ya ce:

"A nawa hangen, yiwuwar samun nasarar gwamnan a Kotun Koli kadan ce, saboda yanzu kotun za ta yi hukunci ne kan hukunci iri daya da kananan kotuna biyu suka yanke.
"Sai dai kuma, hukuncin da kotun Daukaka Kara ta yanke na cewar wai Gwamna Abba ba dan NNPP ba ne, abin argi ne, domin wannan hurumin jam'iyyar ne aka shiga.
"Ke nan, yanke hukuncin kan abin da ba hurumin kotun kararrakin zabe da Kotun Daukaka Kara ba, wani lamari ne da Kotun Kolin kadai za ta iya warware shi."

An kai karar Gwamna Yusuf Majalisar Dinkin Duniya

A wani labarin, kungiyar APC-YBCK ta gudanar da zanga-zanga a ginin Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

A yayin zanga-zagar, sun nemi majalisar ta sanya takunkumi akan gwamantin Abba Yusuf da magoya bayan jam'iyyar NNPP, inda suke zargin ana farmakar fannin shari'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.