Tinubu: Akwai Yiwuwar Ayyuka 1358 Su Tsaya a Dalilin Tsarin da CBN Ya Dauko
- Canjin shugabancin da aka yi a babban bankin Najeriya ya yi sanadiyyar soke tsare-tsaren da aka saba da su
- Dr. Olayemi Cardoso ba zai cigaba da ayyukan kawo cigaba da babban bankin CBN da rika yi a shekarun baya ba
- A lokacin Godwin Emefiele yana ofis, babban bankin kasar ya rika shiga harkokin noma, kasuwanci zuwa lafiya
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - A dalilin matakin da bankin CBN ya dauka na dakatar da tsare-tsaren cigaban al’umma, ayyuka da yawa za su tsaya.
Rahoto daga Leadership ya nuna akwai alamun cewa ayyuka fiye da 1, 358 da ake amfana da su a karkashin CBN za su zo karshe.
Manoma za su biya CBN bashi?
Manoma sama da miliyan 4.6 da su ka amfana da tsare-tsare da yawa daga babban bankin za su biya bashin kudin da aka ba su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bashin da babban bankin na CBN yake so ya karba daga hannun manoma ya kai N5.25tr.
CBN: Cardoso ya bambanta da Emefiele
Dr. Olayemi Cardoso ya nuna ba zai cigaba da abubuwan da Godwin Emefiele ya fito da su ba, zai fi bada karfi a kan harkar kudi.
Emefiele ya fito da tsarin ABP da ya ci N1.09tr domin taimakawa manoma. Jaridar ta cw watakila za ayi ban-kwana da shirin noman.
Sauran tsare-tsaren da aka kashe kudi a kai sun hada da AGSMEIS da MSMEDF, sabon gwamnan bai da niyyar ya cigaba da su.
Katsalandan ko bunkasa tattalin arziki
A lokacin da Muhammadu Buhari yake mulki, bankin CBN ya rika tsoma baki a kan harkokin noma, ma’adanai da kuma kasuwanci.
Kamfonin DisCos masu alhakin raba wutar lantarki sun samu tallafin N254.39bn a karkashin tsarin NEMSF-2 da watakila an tsaida.
Har ila yau, Emefiele ya taimakawa masu harkar fita daga kaya zuwa ketare da sunan shirin EFI sannan an kawo HSIF a bangaren lafiya.
Sababbin Gwamnonin CBN
Dakatar da Godwin Emefiele da cire Adebisi Shonubi da aka yi ne ya ba Olayemi Cardoso damar zama sabon gwamnan bankin CBN.
Bola Tinubu ya nada Emem Nnana Usoro, Muhammad Sani Abdullahi, Philip Ikeazor, da Bala M. Bello a matsayin mataimakan gwamna.
Asali: Legit.ng