Kungiyar TUC Ta Aike da Muhimmin Gargadi Ga Shugaba Tinubu Kan Karin Albashin N35,000
- Ƙungiyar ƴan kasuwa (TUC) ta gargaɗi gwamnatin tarayya da ta gaggauta biyan ma’aikatan gwamnatin tarayya ƙarin albashin su na Naira 35,000
- Ƙungiyar ta ce tana da cikakken bayani cewa ma’aikata sun samu ƙarin na wata ɗaya kacal na watan Satumba
- Ƙungiyar TUC ta bayyana cewa ma’aikata ƙalilan ne aka biya kuɗin a karo na biyu tun bayan da aka fara biyan kuɗin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar ƴan kasuwa (TUC) ta gargaɗi gwamnatin Bola Tinubu da ta gaggauta biyan duk ma’aikatan gwamnatin tarayya ƙarin albashin N35,000.
Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, TUC ta ce an an cimma yarjejeniyar biyan kuɗin ne a wani taro da aka yi bayan cire tallafin man fetur.
"Ka gaggauta biyan ma'aikata": TUC zuwa ga Tinubu
Festus Osifo, shugaban TUC, ya yi wannan gargaɗin ne ga gwamnatin Tinubu a Abuja a ranar Talata, 12 ga watan Disamba a wani taron manema labarai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron ya biyo bayan taron majalisar zartarwa ta ƙasa (NEC) na gaggawa na ƙungiyar.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ƙungiyar ta yi nuni da cewa tana da tabbacin cewa ma’aikata sun karɓi ƙarin albashin wata ɗaya ne kawai a watan Satumba, inda ta ƙara da cewa ma’aikata ƙalilan ne aka biya a karo na biyu.
Osifo ya bayyana cewa:
"Batun bayar da albashin ma’aikata, a rubuce yake cewa sau ɗaya ne kawai aka biya a watan Satumba, amma kamar yadda yake a yanzu, mambobinmu a ma’aikatan gwamnatin tarayya ba a biya su ƙarin albashin N35,000 ba tun watan Oktoba."
"Muna kira ga gwamnati da ta gaggauta biyan duk wasu kuɗaɗe a yanzu. Mun fahimci cewa suna ƙoƙari domin tabbatar da biyan kuɗin, amma mutane ba su shirya su saurari wani uzuri ba."
"Muna buƙatar su gaggauta biyan wannan ƙarin albashin N35,000 zuwa asusun ajiyar banki na ma'aikatan gwamnatin tarayya ba tare da wani uzuri ba."
Tinubu Ya Saɓa Alkawarin da Ya Yi Wa ASUU
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar malaman jami'a ta ASUU ta soki kason da Shugaba Tinubu ya warewa ɓangaren ilmi a kasafin kuɗin 2023.
Ƙungiyar ta bayyana cewa a lokacin yaƙin neman zaɓe Tinubu ya yi alƙawarin warewa ɓangaren ilmi 15%, amma sai ga shi ba a yi hakan ba a cikin kasafin kuɗin na baɗi.
Asali: Legit.ng