An Fara Kai Ruwa Rana Bayan Tinubu Ya Dakatar da Biyan N35k Ga Ma’aikata, NLC Ta Fadi Matakin Gaba
- Kungiyar Kwadago ta NLC, ta yi barazanar tsunduma yajin aiki bayan Gwamnatin Tarayya ta dakatar da biyan ma’aikata kudaden rage radadi
- A watan Satumba ne aka fara biyan ma’aikatan Gwamnatin Tarayya dubu 35 don rage musu radadin cire tallafi
- Legit Hausa ta ji ta bakin wasu ma'aikatan Gwamnatin Tarayya inda su ka koka kan lamarin biyan kudaden
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya sun nuna damuwarsu kan dakatar da biyan kudaden rage tallafi dubu 35.
Shugaba Tinubu ya fara biyan dubu 35 don rage wa ma’aikatan Gwamnatin Tarayya radadin cire tallafin mai a kasar, Legit ta tattaro.
Mene dalilin biyan kudaden ga ma'aikata?
Bayan ma’aikatan sun karbi na wata daya kacal, shugaban bai sake waiwaitarsu ba game da ci gaba da biyan kudaden.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar, ta bayyana cewa za a fara biyan kudaden ne a ranar 1 ga watan Satumba, cewar Punch.
Har ila yau, binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa an biya kudaden ne kawai a watan Satumbar wannan shekara.
Daraktan yada labarai na kungiyar NLC, Benson Upah ya bayyana cewa:
“Wannan ya saba alkawarin da gwamnatin ta yi wa ma’aikata kuma ba za mu amince da shi ba.”
Wane martani NLC ta yi wa Tinubu?
Upah ya ce wannan mataki na gwamnatin zai sa su tsunduma yajin aiki idan har gwamnatin ba ta shawo kan matsalar ba, cewar Politics Nigeria.
Yayin da ya ke magana da Punch, kakakin Akanta Janar na Tarayya, Bawa Mokwa ya bayyana cewa su na kokarin biyan ma’aikatan nan ba da jimawa ba.
Ya ce:
“Ana ci gaba da aikin biyan kudaden, za a biya su, tuni aka riga aka fara aikin biyan kudaden ga ma’aikata.”
Hausa Legit ta ji ta bakin wasu ma'aikatan Gwamnatin Tarayya kan wannan lamari:
Rilwan Abubakar ya ce tabbas tun watan Satumba ba su sake waiwaitarsu ba kuma ga shi yanzu ana watan Disamba.
Ya ce:
"An yi alkawari tun daga Satumba, zuwa yanzu watanni uku kenan, a cikin wata ukun gaba daya watan Satumba aka biya a farkon makon watan Nuwamba.
"Har yanzu akwai bashin watanni biyu kenan, ka ji yadda abin ya ke kuma mutane su na shan wahala saboda yanayin tsadar rayuwa."
Aliyu Dauda wani ma'aikacin lafiya ya ce:
"Dangane da rashin biyan kudaden ya shafi ma'aikata saboda ba su taba zato ba, amma mun samu labarin cewa NLC ta yi zama a yau Talata kan cewa idan ba a biya kudaden na wata biyu ba za su tsunduma yajin aiki."
Ma’aikata dubu 5 za su rasa albashin Disamba
A wani labarin, Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya dubu biyar ne za su rasa albashin watan Disamba da mu ke ciki.
Wannan na zuwa ne bayan an samu matsala a takardun ma’aikatan da ya shafi na daukar aikinsu da kuma na haihuwa.
Asali: Legit.ng