Zargin Rashawa: Hukumar LASTMA Ta Kori Ma’aikata Biyar, Ta Fara Binciken Wasu 14

Zargin Rashawa: Hukumar LASTMA Ta Kori Ma’aikata Biyar, Ta Fara Binciken Wasu 14

  • Akalla ma'aikata biyar ne aka sallama daga aikin gwamnati a hukumar kula da sa ido kan dokokin tuki (LASTMA) a jihar Legas
  • An kori ma'aikatan biyar ne bayan da wani kwamitin ladabtarwa na hukumar LASTMA ya same su da laifukan da suka shafi rashawa
  • Rahotanni sun bayyana cewa hukumar LASTMA na fama da ma'aikatan da ke aikata laifukan da suka shafi cin hanci da rashawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Legas - Hukumar da ke kula da sa ido kan bin dokokin tukin ababen hawa a jihar Legas (LASTMA) ta kori ma'aikata biyar kan zargin cin hanci da rashawa.

Rahotanni sun bayyana cewa hukumar ta kori wasu biyu daban bayan da wani kwamitin ladabtarwa ya same su da laifin kin zama a wajen aikin su.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Lauyoyin arewa fiye da 600 za su maka gwamnatin Tinubu a kotu, sun fadi dalili

LASTMA ta sallami ma'aikata biyar kan rashawa
Ban da mutum biyar da ta kora, LASTMA na bincike kan wasu jami'ai 14 da ake zargin su da aikata laifuka daban-daban. Hoto: @followlastma
Asali: Twitter

Hakan na zuwa kasa da makonni biyu da aka gurfanar da wasu ma'aikata 11 gaban kwamitin ladabtarwa na hukumar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me hukumar LASTMA ta ce kan korar ma'aikatan ta?

Sanarwa daga Darakta hulda da jama'a da watsa labarai na LASTMA, Mr Adebayo Taofiq a ranar Litinin, ta nuna cewa tuni aka ba jami'an biyar takardun sallamar .

Taofiq ya ce har yanzu hukumar gudanarwar LASTMA na yin bincike kan wasu jami'ai 14 da ake zargin su da aikata laifuka daban-daban, kamar yadda ta wallafa a shafinta na X.

Ya yi nuni da cewa a ranar biyar ga watan Disamba ne aka damka takardun sallamar jami'an hukumar biyar a hannunsu.

A karshe Taofiq ya fadi sakon mukaddashin shugaban hukumar LASTMA ga ma'aikatan hukumar da su kasance masu ruko da gaskiya tare da kaucewa karya dokar aikin gwamnatin jihar Legas ba.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya na fama da matsin tattalin arziki yayin da gwamnatin Tinubu ke sharholiya - Rahoto

Jam'iyyar APC ta kori shugaban karamar hukumar Suleja

A wani labari da muka kawo maku a safiyar yau, kwamitin gudanar da aiki na jam'iyyar APC a jihar Niger ya dakatar da shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Suleja, Gambo Ibrahim.

Jam'iyyar ta dakatar da Ibrahim na tsawon watanni uku kan zargin rashin da'a da wuce gona da iri a aikinsa, rahoton Legit Hausa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel