“Yan Sanda Sun Yi Garkuwa da Ni, Sun Karbi Naira Miliyan 1 Kudin Fansa”, Cewar Mr Soyemi

“Yan Sanda Sun Yi Garkuwa da Ni, Sun Karbi Naira Miliyan 1 Kudin Fansa”, Cewar Mr Soyemi

  • Wasu jami'an 'yan sanda sun yi garkuwa da wani mutum da iyalinsa tare da karbar Naira miliyan daya matsayin kudin fansa
  • Mr. Samuel Soyemi ne ya bayar da labarin yadda jami'an suka sace shi daga gidansa da ke jihar Ogun, inda ya ce sun sace wasu kayyaki a gidan
  • Tuni dai Mr Soyemi ya shigar da korafin hakan ga shugaban 'yan sanda na kasa, inda kakakin rundunar ya tabbatar da karbar korafin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Ogun - Wani mutum mai suna Mr. Samuel Soyemi ya labarta yadda wasu mutum biyu da suka yi ikirarin 'yan sanda ne daga shiyya ta 2 a Onikan, jihar Legas suka yi garkuwa da shi da iyalinsa.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Lauyoyin arewa fiye da 600 za su maka gwamnatin Tinubu a kotu, sun fadi dalili

Mr Soyemi ya kalli hakan matsayin garkuwa da mutane da kuma fashi da makami, inda ya ce jami'an sun kwashe naira miliyan daya daga asusunsa kafin suka sake shi da iyalinsa.

An zargi 'yan sanda da yin garkuwa da Mr Soyemi da iyalansa
Soyemi ya ce 'yan sanda sun kwashe Naira miliyan daya daga asusunsa zuwa wani asusun bankin Opay bayan garkuwa da shi da iyalinsa. Hoto: Nigerian Police
Asali: Facebook

Soyemi ya shaidawa da jaridar Punch cewa lamarin ya faru a ranar 10 ga watan Oktoba, inda 'yan fashin suka shiga gidansa da ke Osiele ta Abeokuta, jihar Ogun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ya faru tsakani na da 'yan sanda - Mr Soyemi

A cewarsa, 'yan sandan sun zarge shi da aikata laifukan shan jini da shiga kungiyar asiri, zargin da ya ce babu kamshin gaskiya a ciki.

Mutumin ya kuma labarta yadda 'yan sandan suka kai shi harabar ofishin 'yan sanda na Ifo tare da neman Naira miliyan 10 ko su batar da shi har abada.

Ba tare da shiga cikin ofishin don cike wasu takardu ba, Soyemi ya ce jami'an suka yi nasarar kwashe kudi daga asusunsa zuwa wani asusun bankin Opay.

Kara karanta wannan

Gagaruman abubuwa 3 da za su faru a 2024, malamin addini ya yi hasashe

"A yanzu haka ko abinci ba mu da shi a gida, saboda sai da na ranto kudin da na tura musu a ranar. Sun karbi kayan da sun kai darajar naira miliyan 3 daga hannun mu.
"Na shigar da kara a ofishin 'yan sanda na shiyya ta 2 amma babu abin da suka yi, ina rokon shugaban 'yan sanda na kasa, Kayode Egbetokun ya kawo mun dauki."

A cewar Soyemi.

Kakakin rundunar 'yan sanda FRPO, Adejobi ya tabbatar da korafin da Mr Soyemi ya shigar inda ya ce rundunar na bincike kan wannan danyen aiki da aka aikata wa mutumin.

An samu rahotanni yadda aka cafke wasu jami'an 'yan sanda kan garkuwa da mutane da karbar kudin rashawa, Premium Times ta taba ruwaito irin faruwar hakan a Fatakwal.

Yan sanda sun kama masu laifi 130 a jihar Katsina

A wani labarin kuma, rundunar 'yan sanda ta sanar da nasarar da dakarunta suka samu na afke masu laifi 130 a jihar Katsina, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Daga cikin wadanda aka kama akwai 'yan fashi 38, masu kisan kai 16, da sauransu, kuma ta kubutar da mutum 69.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.