Ba a Gama da Jimamin Kashe Masu Maulidi Ba, ’Yan Bindiga Sun Yi Kazamin Barna a Bauchi
- Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun hallaka dan banga a wani yankin jihar Bauchi, inda suka sace wasu tare da jikkata da dama
- An kuma ruwaito yadda suka yi awon gaba da wasu mutane yayin da suka kai mummunan a yammacin ranar Asabar
- Ya zuwa yanzu, rundunar ’yan sandan jihar bata tabbatar da lamarin ba, duk da cewa shaidu sun tabbatar da harin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Ningi, jihar Bauchi - Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe wani dan banga a kauyen Bakutumbe da ke karamar hukumar Ningi a jihar Bauchi tare da raunata wasu uku, rahoton Punch.
A cewar wata majiya daga yankin da ta nemi a sakaya sunanta, ‘yan bindigar da suka kai farmaki kauyen a yammacin ranar Asabar sun kuma yi awon gaba da wasu mutane hudu.
Majiyar ta bayyana cewa yayin da ‘yan bindigar suka isa kauyen, nan da nan suka fara harbe-harbe domin tsoratar da mazauna kauyen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka kashe dan banga
Ya ci gaba da cewa, ‘yan bindigar sun kashe wani dan banga na yankin, Malam Dan Ladiyo, tare da harbe wasu mutane uku tare da raunata su.
Hakazalika, wadanda suka samu raunuka a harin su ne Habila Garba, Nura Yakubu, da kuma Sam’ana, wadanda a yanzu haka suke samun kulawa a wani asibiti da ke Ningi.
Majiyar ta kara da cewa bayan sun bar kauyen ne suka nufi dajin Lukutu da ke yankin, inda ake kyautata zaton suke fakewa.
‘Yan sanda sun yi martani kan lamarin?
Kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ya ci tura domin jami’in hulda da jama’a Ahmed Wakil bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba.
Har ila yau bai mayar da martani ga sakon tes da aka aike masa ba dangane da aukuwar lamarin mara dadin ji.
Mummunan hari a Taraba
Akalla mutum 33 da suka hada da makiyaya da manoma ne rahotanni suka ce an kashe a hare-haren da aka kai wasu kauyuka uku a karamar hukumar Bali ta jihar Taraba.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa an kashe mutum 21 a ƙauyen Garbatau, 10 a Ganfeto, biyu kuma a Hawan mata, duk a cikin karamar hukuma daya.
Asali: Legit.ng