Innalillahi: Babban Limamin Masallacin Tede Kuma Shugaban Majalisar Malamai Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- An shiga jimami yayin da wani babban limami a garin Tede da ke karamar hukumar Atisbo na jihar Oyo ya rasu
- Marigayin mai suna Alhaji Ahmad Tijani Adedigba kafin rasuwarshi shi ne babban limamin Tede
- Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya nuna alhininsa kan wannan babbar rashi inda ya yi addu’ar Allah ya masa rahama
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo – Babban limamin Tede da ke a cikin jihar Oyo, Alhaji Ahmad Tijani Adedigba ya riga mu gidan gaskiya.
Kafin rasuwar marigayin, shi ne shugaban kungiyar limamai da malamai da ke Oke Ogun.
Martanin Gwamna Makinde kan rasuwar
Yayin da ya ke tura sakon jaje, Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Makinde ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi 10 ga watan Disamba, cewar Independent News.
Gwamnan ya ce tabbas al’ummar Musulmi sun yi babban rashi da rasuwar malamin da ya ba da gudunmawa ga addini.
Sanarwar ta ce:
“Cikin jimami na samu labarin rasuwar Alhaji Ahmad Tijani, shugaban gamayyar limamai da kuma malamai a Tede da ke karamar hukumar Atisbo a jihar.
“Marigayin mutum ne mai son zaman lafiya wanda ya ba da gudunmawa wurin jagorantar limamai da malamai da inganta addini a Oke Ogun.
“Yayin da mu ke mika lamarin mu ga Allah, mu na addu’ar ubangiji ya ba shi aljannar Firdausi da sauran wadanda su ka mutu.”
Dan tsohon Alaafin na Oyo ya rasu
Gwamna Makinde ya ce tabbas al’ummar Musulmi za su yi kewar marigayin musamman irin gudunmawa da ya bayar, cewar Daily Post.
Har ila yau, dan tsohon Alaafin na Oyo, Abdulatai Adeyemi ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da cutar sukari a jihar.
Marigayin wanda aka fi sani da ‘D-Gov’ ya rasu ne a asibitin Jami’ar Ibadan da ke jihar Osun da safiyar Juma’a 8 ga watan Disamba.
Imam Sa’id ya rasu a Gombe
A wani labarin, Allah ya karbi rasuwar babban limamin masallacin Izalah da ke Abuja Low-Coast a cikin garin Gombe.
Marigayin mai suna Imam Sa’id Abubakar ya rasu ne bayan fama da jinya na tsawon lokaci a jihar.
Asali: Legit.ng