Sanatoci Sun Burge, Sun Ba da Albashinsu Gaba Daya Ga ’Yan Maulidin da Harin Soji Ya Shafa
- Gwamnatin jihar Kaduna za ta samu kudaden da za ta rabawa wadanda hadarin kisan kuskure na kare dangi da aka yiwa mazauna Igabi
- Sanatoci sun ba da albashinsu na watan Disamba a matsayin gudunmawar tallafawa ahalin wadanda aka kashe ba tare da wani laifi ba
- Sojoji sun saki bama-bamai kan musulmai masu bikin Maulidi, lamarin da ya jawo cece-kuce da ayar tambaya game a Najeriya
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Jihar Kaduna - Dukkan Sanatocin Najeriya 109 sun amince da ba da gudummawar albashinsu na watan Disamba, ga ahalin wadanda harin kure na sojin Najeriya ya fada musu a makon jiya.
Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa, kudin da sanatocin suka bayar zai kai Naira miliyan 109, wanda ake kyautata zaton zai taimakawa ahalin.
Idan baku manta ba, sojoji sun yi kuskuren sakin bama-bamai kan wasu musulmai masu bikin Maulidi da basu ji ba basu gani ba a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka ba da gudunmawar
Mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau I. Jibrin ne ya sanar da hakan a fadar gwamnatin Kaduna a lokacin da ya jagoranci wata tawagar ‘yan majalisar dattijai zuwa jihar.
Sanatocin sun samu tarba daga gwamnan jihar, Sanata Uba Sani, wanda ya bar majalisa a bana ya kama mulkin jihar da ke Arewa ta Yamma.
Sanata Barau, a wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, ya ce za a aike da kudin ne ga gwamnan jihar domin kai wa wadanda abin ya shafa.
Sakon godiya a madadin ahalin
Gwamnan ya godewa sanatocin da suka bayar da wannan tallafi, tare da bayyana jin dadinsa da kawo tallafi da tausayawa wadanda abin ya shafa, rahoton NTA.
Tawagar majalisar dai na kunshe da masu ruwa da tsaki da masu fada a ji a kasar nan, ciki har da sanata Ali Ndume, Abba Moro da dai sauransu.
Ba wannan ne karon farko da ake yiwa mazauna Arewacin Najeriya irin wannan kisa da sunan kuskure ba, hakan ya sha faruwa kuma an kashe mutane da yawa.
A nemo wadanda sila aikata, inji Atiku
A wani labarin, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da kisan masu Maulidi a jihar Kaduna.
Atiku ya bukaci ayi kwakkwaran bincike don tabbatar da zakulo wadanda su ka aikata wannan aika-aika.
Asali: Legit.ng